Da duminsa: AGF Malami yayi wuff da diyar shugaba Buhari, hotuna suna bayyana

Da duminsa: AGF Malami yayi wuff da diyar shugaba Buhari, hotuna suna bayyana

  • Ministan shari'a na Najeriya, AGF Abubakar Malami yanzu ya zama daya daga cikin sirikan shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Malami ya aura daya daga cikin 'ya'yan shugaban kasa Muhammadu Buhari, nana Hadiza, a Aso Rock a ranar Juma'a, 8 ga Yuli
  • Hadiza a baya ta taba auren Abdulrahman Mamman Kurfi wanda bincike ya bayyana cewa suna da 'ya'ya shida da shi

A yau ranar 8 ga watan Yulin 2022 ne aka daura auren Nana Hadiza Muhammadu Buhari da AGF Abubakar Malami, SAN.

An daura auren a Abuja yayin da aka yi karamin biki a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake Abuja tare da 'yan uwa da abokan arziki.

Hadiza Buhari
Da duminsa: AGF Malami yayi wuff da diyar shugaba Buhari, hotuna suna bayyana. Hoto daga @arewafamilyweddings
Asali: Instagram

Daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan.

"Eh, da gaske ne, antoni janar na tarayya ya aura diyar shugaban kasa."

Kara karanta wannan

Harin gidan yarin Kuje: Buhari na ganawa da shugabannin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyin sun yi ikirarin cewa, duk da an yi karamin biki bayan daurin aue, an kammala babu wasu hayaniya ko hargitsin shagulgula.

Nana Hadiza diyar marigayiya Safinatu ce, matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta farko.

Ta taba auren Abdulrahman Mamman Kurfi kuma suka abu bayan haifar 'ya'ya shida da suka yi.

Hadiza yanzu ita ce matar Malami ta uku bayan Aisha ta farko da Fatima ta biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng