Aikin Hajji :Jami’in NAHCON ya karkatar da kudin maniyyata a Neja

Aikin Hajji :Jami’in NAHCON ya karkatar da kudin maniyyata a Neja

  • Maniyyata da dama daga karmar hukumar Bida a jihar Neja baza su samu zuwa aikin hajjin bana saboda Jami’in NAHCON ya karkatar da kudin maniyyata a Neja
  • Hukumar NAHCON na jihar Neja ta ce ta samu kora-korafen maniyyata da yawa akan rashin tafiya aikin hajji bayan sun biya kudin su
  • NAHCON ta kafa kwamitin binckiken jami’in Alhazai na yankin Bida akan miliyoyin kudin maniyyata da aka biya a asusunsa bankin sa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Neja : Maniyyatan daga karamar hukumar Bida ta jihar Neja ba za su yi aikin Hajjin bana ba saboda jami’in Alhazai na yankin (APO), Nma Ndagana, ya kasa bayyana miliyoyin kudi da aka biya a asusunsa bankin sa.

Jaridar Daliy Trust ta tattaro cewa kimanin mahajjata 150 ne suka biya kudi a asusun bankin APO kamar yadda ya umarce su a maimakon su biya a asusun da hukuma ta kebe na bankin Jaiz.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Tashi ya gagara, alhazan Neja 2,265 sun shiga zulumi da takaici

Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Neja, Alhaji Umar Maku Lapai, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni aka kafa kwamitin da zai binciki zargin rahoton Daily Trust.

Hajji
Aikin Hajji :Jami’in NAHCON ya karkatar da kudin maniyyata a Neja : Foto Leadership News
Asali: UGC

Sai dai bai fadi adadin maniyyatan da abin ya shafa ba, inda ya bayyana cewa an samu korafe-korafe da dama, kuma har yanzu mutane suna ci gaba da gabatar da irin wadannan korafe-korafen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce adadin mutane da APO ya karbi kudin su, sun fi adadinn kujerun maniyyata da hukumar NAHCON ta ware wa karamar hukumar sa.

“Yadda ake abun ya rabu kashe biyu . Mu a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Neja mun biya kudin mutane 2,265 amma har yanzu ba mu samu cikakkiyar takardar biza ba. Hukumar Alhazai ta Najeriya ce ke da alhakin ba mu biza.

Kara karanta wannan

Duk daya muke: Kristoci sun taya musulmai cire ciyayi a masalacin Kaduna.

“Abun dake faruwa Bida shine, adadin maniyyatan da ya yi wa rajista (APO) sun zarce adadin da aka ce ya yi wa rajista. Wadanda ya biya mana kudadensu an ba su biza. Wadanda suka biya kudinsu a asusunsu bankin sa na kade ke da matsala.
“Mun kafa kwamiti bincike dan gano ainihin abin da ya faru. Kwamitin na ci gaba da bincike. mutanen da abin ya shafa. Da farko mun yi rajistar masu korafe-korafe 28. Daga baya kuma mutane da yawa suka cigaba da zuwa,” inji shi.

Lapai ya kuma bayyana cewa idan har aka gano gaskiya ne, ba za a bar jami’in ya yi tafiya ba, kuma hukuma ba za ta dauki nauyin biyan kudaden da ake biya a asusun daidaikun mutane ba.

Sai dai bai bayyana inda APO yake.

Sai dai wani jami’n hukumar,ya shaida wa wakilan Daily Trust cewa APO yana hannun yansanda kuma ana yi masa tambayoyi

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Duk daya muke : Kristoci sun taya musulmai cire ciyayi a masalacin Kaduna

A wani labarni, Wasu mabiya addinin Kirista a karamar hukumar Kachia dake kudancin jihar Kaduna sun taya musulmi yanke ciyawa a wani masallaci da ake yin sallar idi.

Mista Daniel Bitrus, shugaban tawagar kristocin da suka ta ya musulmi gudanar da wannan aikin, ya ce sun yi hakan ne domin karfafa zumunci, hakuri da zaman lafiya da juna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel