Yanzu-Yanzu: Watanni Bayan Rasuwar Sarkin, Daya Cikin Matar Alaafin Na Oyo, Ta Rasu

Yanzu-Yanzu: Watanni Bayan Rasuwar Sarkin, Daya Cikin Matar Alaafin Na Oyo, Ta Rasu

  • Olori Kafayat, matar marigayi, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi ta hudu ta riga mu gidan gaskiya yan watanni bayan rasuwar sarkin
  • Mai magana da yawun fadar Alaafin na Oyo, Mr Bode Durojaye, ta tabbatar da rasuwarta a Amurka amma bai bada cikakken bayani ba
  • Marigayiya Kafayat Adeyemi, ita ce mahaifiyar Yarima Adebayo Adeyemi (D'Gov), wanda shine shugaban hukumar fanso na Jihar Oyo

Jihar Oyo - Kimanin watanni biyu bayan rasuwar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III, daya cikin matansa, Olori Kafayat, ta rasu a ranar Juma'a, Leadership ta ruwaito.

Duk da cewa ba a samu cikakken bayani kan mutuwarta ba amma majiyoyi sun ce ta rasu ne a daren ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Babban ɗan shugaban Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya rasu

Alaafin of Oyo.
Watanni Bayan Rasuwarsa, Matar Alaafin Na Oyo, Kafayat Ta Rasu. @MobilePunch.
Asali: UGC

Mai magana da yawun fadar Alaafin ya tabbatar da rasuwarta

Direkatan Watsa Labarai a Fadar Alaafin, Mr Bode Durojaye, ta tabbatar da rasuwarta ga The Punch a safiyar ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Eh, Ta mutu a Amurka. Zan bada karin bayani anjima."

Oba Adeyemi ya rasu ne a ranar Juma'a 22 ga watan Afrilu a Asibitin Koyarwa ta Afe Babalola, Ado Ekiti, bayan gajeruwar rashin lafiya yana da shekaru 83.

Kawo yanzu Oyo ba ta zabi wani Alaafin ba bayan rasuwar Oba Adeyemi'

Olori Kafayat Adeyemi, wacce ita ce matar marigayin sarkin Oba Adeyemi III ta hudu, ita ce mahaifiyar Yarima Adebayo Adeyemi (D'Gov), wanda shine shugaban hukumar fanso na Jihar Oyo.

Kafin rasuwarta, ana kiran ta Iya Aguo ko Iya Ibeji a masarautar Oyo.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi dirama a majalisa, tsakanin Ahmad Lawan da Okorocha

A wani rahoton, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel