Babban Ɗan Farfesa Ango Abdullahi Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Babban Ɗan Farfesa Ango Abdullahi Ya Rigamu Gidan Gaskiya

  • Shugaban ƙungiyar Dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya yi rashin babban ɗansa, Isa Ango Abdullahi jiya Alhamis da yammaci
  • Bayanai daga Zariya sun tabbatar da cewa za'a dawo da gawarsa daga birnin tarayya Abuja yau Jumu'a domin yi masa Jana'iza
  • Kafin rasuwarsa, Marigayi Isa ma'aikaci ne a hukumar adana bayanan fasaha (NIA) ta ƙasa da ke birnin Abuja

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zaria, jihar Kaduna - Shugaban ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, Farfesa Ango Abdullahi, ya yi rashin babban ɗan sa, Isa Ango Abdullahi, bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Wata majiya daga iyalan gidan Ango Abdullah ce ta tabbatar da rasuwar ga wakilin jaridar Daily Trust a birnin Zariya, jihar Kaduna, ranar Jumu'a.

Isah Ango Abdullahi.
Babban Ɗan Farfesa Ango Abdullahi Ya Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewa Isah ya rasu ne da yammacin ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, 2022 a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi dirama a majalisa, tsakanin Ahmad Lawan da Okorocha

Ya ƙara da cewa ana tsammanin za'a dawo da gawarsa gida a nan Zariya yau Jumu'a domin yi mata Jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar majiyar da jaridar ta samu, za'a yi wa mamacin Sallar Jana'iza ne a babban Masallacin Jumu'a na Haruna Ɗanja da misalin ƙarfe 1:30 na rana.

Kafin rasuwarsa, Marigayi Isa Ango Abdullahi, ma'aikaci ne a hukumar tattara bayanan fasaha (NIA) a birnin tarayya Abuja.

Haka nan kuma ya rasu ya bar mata guda ɗaya da kuma 'ya'ya, Allah ya jikansa ya gafarta masa kurakuransa.

Yar Najeriya da taje aikin Hajji ta rasu a Saudiyya

A wani labarin kuma kun ji cewa Wata Hajiya yar Najeriya, Hajiya Aisha Ahmad, ta rigamu gidan gaskiya a ƙasar Saudiyya

Wata yar Najeriya da ta yi niyyar aikin Hajjin bana 2022, Hajiya Aisha Ahmad, ta rigamu gidan gaskiya sanadin rashin lafiya a Saudiyya ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sanata Ekweremadu ya bayyana a gaban Kotun Birtaniya kan tuhumar yanke sassan jiki

Aisha Ahmad, daga ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa , ta rasu ne bayan kamuwa da gajeruwar rashin lafiya, a cewar Alhaji Idris Al- Makura, shugabann hukumar jin daɗin Alhazai na jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel