Zabe: INEC ta shiga damuwa kan yadda ba a karbar katunan zabe gabanin 2023

Zabe: INEC ta shiga damuwa kan yadda ba a karbar katunan zabe gabanin 2023

  • Yayin da zaben 2023 ke gabatowa, jihar Legas ta shirya wani shirin wayar da kan masu kada kuri'u
  • Wannan shiri an yi shi ne da nufin wayar da kan masu kada kuri'a su fahimci inda aka dosa a zaben na 2023
  • Ya zuwa yanzu, hukumar INEC ta bayyana yawan masu karbar katin zabe, inda ta koka da cewa ya yi matukar kankanta

Jihar Legas - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun karancin karbar katin zabe na dindindin a jihar Legas.

Kwamishinan zabe na jihar Mista Olusegun Agbaje ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na mazabu na shekara-shekara na takwas da aka gudanar ranar Alhamis a Legas.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

INEC ta koka da yadda ake karbar katin zabe
2023: INEC ta shiga damuwa kan yadda 'yan Najeriya ba sa karbar katunan zabensu | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Legas ce ta shirya taron kan muhimmancin katin zabe na PVC gabanin babban zabe na 2023.

Taron dai yana gudana ne a lokaci guda a mazabu 40 na jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Agbaje ya samu wakilcin wani jami’in INEC ne Mista Emmanuel Adegboyega, a yayin taron da aka gudanar a mazabar Eti-Osa II.

Agbaje ya ce:

“Rashin yawan karbar PVC a jihar Legas abin damuwa ne saboda PVC 6,382 ne kawai daga cikin 34,242 da aka karba daga hedikwatar hukumar na zangon farko da na biyu na CVR.
“Wannan 18.6% ne kawai; Hakazalika, ga tsoffin PVCs, jimillar 1,091,157 har yanzu masu su ba su karba ba.”

Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su wayar da kan masu kada kuri’a kan kamar yadda dokar zabe ta 2022 da 1999 suka tanada.

Kara karanta wannan

Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi

A cewarsa, wayar da kan jama'a kan lamarin na da matukar muhimmanci ga zaben 2023 mai zuwa.

Manufar shirin

Tun da farko, dan majalisa mai wakiltar mazabar Eti-Osa II, Mista Gbolahan Yishawu, ya ce manufar shirin kamar taron zauren gari ne na filin fadi ra’ayoyinka.

Yishawu ya ci gaba da cewa:

“Taron fadi ra'ayinka na nufin tattara tunanin jama’ar mazabar ka, kuma taken taron shi ne fifita batun babban zaben 2023, muhimmancin PVC.
“Muna kokarin wayar da kan jama’ar mu ne don tabbatar da cewa sun je sun yi rajista ba wai kawai rajista ba, su karbi katin zaben su.
“Kun ga sadda na gudanar da wani atisaye na kokarin gano zahirin wadanda suka yi rajista kuma suka karbi PVC."

Zaben 2023: APC za ta kaddamar da tashar yanar gizo da za ta sa a dama da matasa a siyasa

A wani labarin, jam’iyyar APC mai mulki ba shirya wasa ba, domin ta shirya kaddamar da shafin yanar gizo domin hada kan matasa kafin zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Tallafin fetur: Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari, ta ce an sace Naira Tiriliyan 2.9

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya bayyana shirin ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni a Abuja.

Mista Israel ya bayyana cewa sabon shirin an yi shi ne domin tabbatar da damawa da matasa a harkokin siyasar jam'iyyar. Ya ce dandali ne da ake son amfani dashi wajen jawo hankalin matasa zuwa jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel