Da duminsa: Majalisar Dattawa ta Aike Wakilai UK Kan Kamen Sanata Ekweremadu

Da duminsa: Majalisar Dattawa ta Aike Wakilai UK Kan Kamen Sanata Ekweremadu

  • Majalisar dattawa ta bayyana aika wakilai zuwa kasar Burtaniya don ganin halin da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan, Ike Ekwdremadu ke ciki
  • Ahmad Lawan ya ce, wakilan sun kunshi mambobin kwamitin kula da lamurran waje wadanda zasu tafi birnin London ranar Juma'a kan lamarin
  • Haka zalika, ya tabbatarwa iyalinsa da sauran 'yan Najeriya cewa zasu cigaba da kai masa agajin da ya dace don tabbatar da an yi adalci kan lamarinsa

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta ce zata tura wakilanta zuwa Burtaniya don ganin halin da tsohon mataimakin shugaban majalisar, Ike Ekwdremadu, wanda ake tuhumarsa da yunkurin cire sassan jikin yaro a Turai.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan ranar Laraba bayan majalisar dattawan ta fito daga ganawar sirri, wanda ya dauki tsawon awa guda.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Buhari ya gaza bibiyar kalamansa da aiki, 'Dan majalisar wakilai na APC

Sanata Ike Ekweremadu da Matarsa
Da duminsa: Majalisar Dattawa ta Aike Wakilai UK Kan Kamen Sanata Ekweremadu. Hoto daga vanguardnewsngr.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lawan ya ce wakilan, wadanda suka hada da 'yan kwamtin kula da lamurran waje na majalisar dattawan zasu je birnin London ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

Haka zalika, shugaban majalisar dattawa ya kafa kwamitin da zasu je babban kotun Burtaniya don samun karin bayani game da lamarin.

Ya ce ministan kula da lamurran waje, Geoffrey Onyeama yana iya kokarinsa don agazawa Ike Ekwdremadu da matarsa, Beatrice.

Lawan ya ce majalisar dattawa ta yanke shawarar gajarta lamarin saboda lamarin na gaban kotu yanzu haka.

Saboda haka, ya tabbatar wa iyalin Ekweremadu da 'yan Najeriya cewa majalisar dattawa zata cigaba da hada kai da ministan kula da lamurran waje da babbar hukumar shari'ar Najeriya zuwa Landon kan lamarin.

Manyan Sirruka Sun Sake Bayyana Kan Yaron Da Ekweremadu Ya Kai UK Don Cire Masa Koda

Kara karanta wannan

Bawa kai kariya: Gwamna Matawalle ya kaddamar da kwamitoci, ya rarraba motoci da babura

A wani labari na daban, bayanai game da David Ukpo Nwanmini, yaron da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekwdremadu da matarsa, Beatrice suka kai Amurka don harkallar cire sassan jikin 'dan adam.

Kamar yadda wani wanda ya san yaron wanda 'dan kasuwa ne kuma mai gyaran na'urar komfuta, Oyekan Tobi ya bayyana, ya tabbatar da cewa yaron yafi shekaru 15.

Jaridar Vanguard ta ruwaito yadda Tobi, wanda tsohon dalibin cibiyar jaridancin Najeriya ta Ogba a Legas ne, ya yi jawabi bayan fasfotin yaron da ake zargin shekararsa 15 ya yu yawo a yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel