Manyan Sirruka Sun Sake Bayyana Kan Yaron Da Ekweremadu Ya Kai UK Don Cire Masa Koda

Manyan Sirruka Sun Sake Bayyana Kan Yaron Da Ekweremadu Ya Kai UK Don Cire Masa Koda

  • Manyan bayanai sun cigaba da bayyana kan yaro da Sanata Ike Ekweremadu ya kai Amurka don cire wani sashi na jikinsa
  • Kamar yadda wani 'dan kasuwa kuma mai gyaran na'urar komfuta, Oyekan Tobi ya bayyana, yaran da aka kama na taya 'dan uwansa kasuwanci ne a kasuwar Ikotun
  • Yayin cigaba da bayani, ya ce yaron ya fi shekaru 15 kamar yadda wasu gidan jaridu da hukumomin Amurka suka ruwaito

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bayanai game da David Ukpo Nwanmini, yaron da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekwdremadu da matarsa, Beatrice suka kai Amurka don harkallar cire sassan jikin 'dan adam.

Kamar yadda wani wanda ya san yaron wanda 'dan kasuwa ne kuma mai gyaran na'urar komfuta, Oyekan Tobi ya bayyana, ya tabbatar da cewa yaron yafi shekaru 15.

Eke Kweremadu da Matarsa
Manyan Sirruka Sun Sake Bayyana Kan Yaron Da Ekweremadu Ya Kai UK Don Cire Masa Koda. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito yadda Tobi, wanda tsohon dalibin cibiyar jaridancin Najeriya ta Ogba a Legas ne, ya yi jawabi bayan fasfotin yaron da ake zargin shekararsa 15 ya yu yawo a yanar gizo.

Kamar yadda ya bayyana, yaron dake jikin fasfotin mai suna David, 'dan asalin jihar Ebonyi ne wanda ke taimaka wa yayansa Linus ( wanda aka fi sani da) Mile 2, kasuwanci wajan nemo masa kwastomomi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa: "Yayan nasa na kasuwancin da ya shafi kayayyakin waya, kuma ba gaskiya bane a ce shekarun yaron 15, saboda yaron mai shekaru 15 bai da karfin janyo kwastomomi a kasuwa tare da wasu yara. Ba yaro bane wanda zaka dallawa mari a hanya ka tafi lami lafiya. Saboda haka, ya kamata a ce yana shekaru 20 da wani abu".

Yayin cigaba da jawabi, ya fallasa yadda aka dauki tsawon lokaci ba a ganinsa cikin 'yan uwansa biyu a kasuwar.

"Suna sayar da kayayyakin waya a kan baro wuraren kasuwar Ikotun.
"Babban wansu, Linus shi ma a da yana sana'ar sai dai kayyakin waya a kan baro, daga bisani ya daina gami da bude shagon sai da kayayyakin.

"Sannan ya janyo kannensa uku, wanda David na daya daga cikinsu don su cigaba da jan ragamar sai da kayayyakin wayar a kan baro."

Asali: Legit.ng

Online view pixel