Kano: Mazauna Kofar Nasarawa Sun Koka Kan Yadda Ake Rushe Ajujuwa Ana Gina Shaguna

Kano: Mazauna Kofar Nasarawa Sun Koka Kan Yadda Ake Rushe Ajujuwa Ana Gina Shaguna

  • Mazauna Kano sun koka a kan yadda ake kokarin kwace makarantar sakandirin Kofar Nasarawa, wacce aka fi sani da GSS K/Nasarawa
  • An ruwaito yadda aka rushe wasu azuzuwa da katangar bayan makarantar don mai da wurin harabar kasuwanci tare da shimfida ginin shagunan
  • Hakan yasa mazauna yankin shiga cikin damuwa, duba da yadda makarantar ta kasance daya daga cikin dadaddun makarantu a jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Mazauna Kano sun koka kan yadda ake ta shiga filin makarantar Sakandaren gwamnati dake Kofar Nasarawa, wacce aka fi sani da GSS K/Nasarawa inda yanzu haka aka fara rsuhe ajujuwa domin gina shaguna.

Mazauna da kungiyoyi masu zaman kansu a cikin birnin suna cigaba da kokawa bisa yadda ake gina shaguna a filayen da suke mallakin asibitoci, masallatai, filayen kwallo da sauran su.

Kara karanta wannan

Borno: 'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai

An tattaro rahotanni a kan yadda aka saida wasu azuzuwa da katangar bayan makarantar gwamnati ta Kofar Nasarawa, wadanda suke kusa da gidan wasan Sani Abacha ga mutanen don gina shagunan.

Gwamna Ganduje na Kano
Kano: Mazauna Kofar Nasarawa Sun Koka Kan Yadda Ake Rushe Ajujuwa Ana Gina Shaguna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan katangar makarantar ya ratsa ta sanan nan titin IBB kusa da kasuwar Kwari, wanda ake ganin shine dalilin siyar da wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da Daily Trust ta ziyarci makarantar jiya, an gano yadda aka shimfida ginin shagunan, wanda motar rusa gini ta rusa wasu bangaren tsoffin azuzuwan makarantar.

Wani 'dan kasuwa kusa da makarantar ya shaida yadda aka rushe wasu azuzuwa baya ga bangon bayan makarantar.

"Mu dai kawai mun ga motar rushe gini tana rushe ginin, inda wasu ke gyarawa gami da shimfidar gini. Maganar gaskiya, ba mu yi tunanin za a kai wannan matakin ba," a cewarsa.

Daily Trust ta tattaro yadda makarantar ta kasance daya daga cikin dadaddun makarantu a birnin, yayin da mazauna yankin suka ji tsoro yadda tarihinta ke kokarin rushewa bisa yadda aka mallake wani bangarenta.

Kara karanta wannan

Zunuban Ike Ekweremadu: Manyan rigingimu 4 da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya fada ciki

"Wannan tsohuwar makaranta ce. Dukkanmu mun taso mun ga makarantar a nan ne. Amma yau, suna son gurgunta cigabanta," a cewar wani mazaunin yankin, Jamilu Saad.

Yayin da ake ta yada cewa gwamanati ta kwace filin don gina shagunan, tare da ikirarin kuskure ne yin ginin, Daily Trust bata samu wani ma'aikacin gwamnati da zai tabbatar da hakan ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.

‘Yan kasuwa sun fito zanga-zanga domin hana Gwamnatin Ganduje kara shaguna a Wambai

A wani labari na daban, ‘yan kasuwan Kofar Wambai sun buge da zanga-zanga a garin Kano a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, a dalilin shirin kafa wasu shagun.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa jama’a sun tashi da safe ne kurum suka ga ana aikin gina shagunan da za a raba ta kan hanyoyin da ake wucewa.

Masu zanga-zangar sun taru a layin Sani Buhari domin nuna rashin amincewarsu. A gefe guda kuma jami’an ‘yan sanda sun yi ta kokarin su tarwatsa su.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Sake Jaddada Cewa Sai An Ladabtar Da 'Yan Ta'adda, Ya kwatantasu da Ragwaye

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel