Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 11, Sun Kallafawa Wasu Harajin Noma

Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 11, Sun Kallafawa Wasu Harajin Noma

  • Hatsabiban miyagun 'yan bindiga sun kutsa kauyen Gandhi dake karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto inda suka halaka manoma
  • Sun tarar da manoma a gonakinsu inda suka halaka har 11 a take ba tare da laifin zaune balle na tsaye ba a kauyen Kuryar da wani mai makwabtaka da shi
  • Mazauna yankunan sun bayyana cewa, 'yan bindiga sun kallafa musu haraji wanda zasu biya idan suna son yin noma

Rabah, Sokoto - 'Yan bindiga sun halaka manoma 11 a yankin Ghandi dake karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto.

Kamar yadda bincike ya nuna, harin ya faru wurin karfe 12 na ranar Asabar.

Wata majiya tace wadanda lamarin ya ritsa dasu suna aiki ne a gonakinsu yayin da aka kai musu farmakin.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda, Shaguna da Gidaje a Bukkuyum

Taswirar jihar Sokoto
Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 11, Sun Kallafawa Wasu Harajin Noma. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun riske su a gonakinsu kuma suka kashesu babu dalili," sakataren hakimin Ghandi, Tukur Muhammad, ya sanar da Daily Trust.

'Yan bindigan sun yi yunkurin garkuwa da wasu manoman amma 'yan sa kai suka bankado shirinsu.

Muhammad ya bayyana cewa, takwas daga cikin manoman an kashe su a kauyen Kuryar yayin da uku aka halaka su a kauye mai makwabtaka.

"Basu son mu yi aiki a gonakinmu. A kowacce rana suna kai wa manomanmu farmaki. Sun kuma bukaci sauran kauyukan da su biya haraji kafin su bar su yin noma duk da ba da wannan muka dogara ba a yankinmu," yace.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, ya ce yana kan hanya ne amma zai bincika kuma ya kira, wanda har a lokacin rubuta wannan rahoton bai yi ba.

Kara karanta wannan

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda, Shaguna da Gidaje a Bukkuyum

A wani labari na daban, 'yan bindiga a ranar Alhamis sun kone ofishin 'yan sanda, shaguna da gidaje uku a kauyen Zugu dake karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Sai dai, wani shugaban matasa a Bukkuyum, Abubakar Garba, yace babu wanda aka kashe a farmakin, Premium Times ta ruwaito.

Yace bayan harin, mazauna yankin da yawa sun yi gudun hijira zuwa Bukkuyum da sauran kauyukan dake karamar hukumar Gummi ta jihar. Zugu shine kauye na biyu a girma a karamar hukumar Bukkuyum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel