Dalilan da suka sa ba zan iya biyan ma'aikatan jihata Albashi ba, Gwamna Ortom

Dalilan da suka sa ba zan iya biyan ma'aikatan jihata Albashi ba, Gwamna Ortom

  • Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce ya zama abu mai wahala biyan ma'aikatan jihar Albashi
  • Rahoto ya nuna cewa ma'aikatan jihar sun jima suna koka wa kan rashin biyansu Albashi tsawon watanni uku kenan
  • Ortom ya ce rashin tsaro ya hana tattara kuɗin harajin cikin gida, NNPC ba ta iya taɓuka komai, ga kuma nauyi ya yi wa gwamnati yawa

Benue - Gwamna Samuel Ortom ya bayyana cewa abu ne mai matuƙar wahala gwamnatinsa ta iya biya Albashin ma'ikatan jihar Benuwai.

Daily Trust ta ruwaito cewa ma'aikatan da ke aiki ƙarƙashin gwamnatin jihar Benuwai na ta ƙorafin cewa har yanzu suna bin bashin albashin watanni uku.

Gwamna Ortom, yayin amsa tambayoyin yan jarida a Makurɗi, babban birnin jihar, ranar Laraba ya faɗi dalilai uku da suka jawo rashin biyan Albashin.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Jirgin sama ɗauke da mutane sama da 100 ya kama da wuta yayin sauka

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.
Dalilan da suka sa ba zan iya biyan ma'aikatan jihata Albashi ba, Gwamna Ortom Hoto: Benue Info/facebook
Asali: Facebook

Ya ɗora laifin kan abubuwa da suka haɗa ƙarin nauye-nauye, gazawar kamfanin mai na kasa NNPC wajen samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya da ƙarancin harajin cikin gida (IGR) sakamakon rashin tsaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya ce abu ne mai matuƙar wahala tattara harajin cikin gida saboda taɓarnarewar tsaro wanda ya maida miliyoyin mutane suka koma yan gudun hijira.

A kalamansa, Gwamna Samuel Ortom ya ce:

"Duk da gwamnatin tarayya na iya ciyo bashi domin ta biya ma'aikata Albashi amma mu a jihohi ba mu da wannan ƙarfin ikon yin haka."
"Ba zamu iya ciyo bashi ba sai da izinin sashin kula da karɓo bashi na ma'aikatar kuɗi ta tarayya (DMO). Ƙalubale ne babban domin muna fuskantar zahirin tattalin ariki."

A wani labarin kuma Gwamnan Bauchi da wani babban Jigon PDP sun sa labule da Wike a Patakwal

Kara karanta wannan

Hajji 2022: Sabon rikici ya ɓalle a gwamnatin Kano, Hadimin Ganduje na zargin kwamandan Hisbah

Rahoto ya nuna cewa manyan jiga-jigan APC na gudanar da taron cikin sirri, babu tabbacin abinda suke tattauna wa.

Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya kai wa Wike ziyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel