Hadimin Ganduje ya caccaki kwamandan hukumar Hisbah kan kujerun Hajji

Hadimin Ganduje ya caccaki kwamandan hukumar Hisbah kan kujerun Hajji

  • Wani rikici ya kunno kai tsakanin jami'an gwamnatin jihar Kano kan wasu kujerun hajji da aka ware wa hukumar Hisbah
  • Hadimin Ganduje, Mujittaba Rabiu Baban Usman, ya zargi Sheikh Ibn Sina da raba wa iyalansa wasu kujerun gwamnati
  • Kwamandan ya musanta zargin, a halin yanzun za'a gudanar da bincike don gano ainihin abinda ya faru

Kano - Rikici ya ɓalle a gwamnatin jihar Kano yayin da aka zargi kwamandan rundunar Hisbah, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina, da yin sama da faɗi da wasu kujerun hajjin bana 2022.

A ruwayar Sahelian Times, an fara saɓanin ne kan kujerun da gwamnatin jihar Kano ta ware wa hukumar yan sandan Musulunci wato Hisbah.

Kwamandan Hisbah, Sheikh Ibn Sina.
Hadimin Ganduje ya caccaki kwamandan hukumar Hisbah kan kujerun Hajji Hoto: Leadership.ng
Asali: UGC

Wani bincike ya nuna cewa babban mai taimaka wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin hukumar Hisbah, Mujittaba Rabiu Baban Usman, ya zargi kwamanda Janar na Hisbah da raba wa iyalansa kujerun da gwamnati ta ware wa jami'anta na hukumar.

Kara karanta wannan

Gagarumar Nasara: Gwamnan Arewa ya ceto rayuwar mutane 3,000 da 'yan bindiga suka sace a jiharsa

A wata tattauna wa Hadimin gwamnan ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina ɗaya ɗaga cikin mutum 7 waɗan da suka kai Fasfo ɗin su a sahun farko don yi mana Visa ta aikin Hajji. Amma a wurin wani taro da muka yi ranar Litinin yayin kiran sunayen waɗan da zasu tafi ƙasa mai tsarki sai aka nemi sunana aka rasa."
"Da na nemi jin dalili, sai aka faɗa mun cewa kwamanda ne ya kawo sunan matarsa, ɗan uwansa da kuma SSA dinsa, da aka nemi dole ya cire ɗaya sai ya bar matarsa da ɗan uwansa."

Wane hali ake ciki kan haka yanzu?

Hadimin gwamnan ya ce lokacin da ya nemi jin abinda ya sa aka cire sunansa daga wurin Ibn Sina, sai ya faɗa masa cewa zai nemi ƙarin kujeru daga hannun Ganduje kuma za'a maida sunansa.

Kara karanta wannan

An gano gawar wata mata cikin yanayi a Abuja, wasu abu biyu na kusa da ita sun ɗaga hankulan mutane

A ɓangarensa, kwamandan Hisbah, Sheikh Ibn Sina, ya musanta zargin da cewa hukumar Alhazai ta jiha ce ta maye gurbinsa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Hakanan da yake martani kan lamarin, shugaban majalisar daraktocin hukumar, Sheikh Shehi Shehi, ya yi alƙawarin gudanar da bincike kan yadda aka maye gurbi ba tare da bin matakai ba.

A wani labarin kuma Majalisar Dattawa ta sa ranar fara tantance sabbin Ministoci 7 da Buhari ya naɗa

Majalisar Dattawan tarayyan Naje r iya ta ce zata tantance sabbin ministocin da shugaba Buhari ya aike mata a mako mai zuwa.

Shugaban majalisar, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, wanda ya sanar da haka ya ce zasu tantance mutanen ne ranar Laraba mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel