An kashe akalla mutum 16 a sabon harin da aka kai jihar Benue

An kashe akalla mutum 16 a sabon harin da aka kai jihar Benue

  • Wasu tsagerun yan bindiga dadi sun sake kai hari jihar Benue kuma an yi rashin rayuka 16
  • Shugaban karamar hukumar da aka kai harin yayi zargin cewa makiyaya ne suka kai musu hari
  • Har ila yau, jihar Benue da wasu jihohin Najeriya na fama da matsalar yan bindiga masu garkuwa da mutane

Benue -Akalla dilolin katako timba guda goma sha shida suka rasa rayukansu a sabon harin da yan bindiga suka kai Mbagwen a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.

Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, wanda ya tabbatar da kisan yace kimanin karfe 7 na yammacin Litinin yan bindiga suka kai hari garin Mbagwen kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi, rahoton Leadership.

Yace:

"An kashe dilolin timba 16, mun tsinci gawawwaki biyar cikin mutum 16."

Kara karanta wannan

Katsina: Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Kashe Mutum 3, Sun Tafi Da Matar Aure

"Mafi akasarin wadanda aka kashe dilolin Timba ne a ranar Litnin yayinda suka je yankar itace a dajin Mbagwen kuma yayinda suke kokarin fita aka bude musu wuta."

Ya ce sun kai kara wajen yan sanda don gudanar da bincike kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Benue
An kashe akalla mutum 16 a sabon harin da aka kai jihar Benue
Asali: Twitter

Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Kashe Mutum 3, Sun Tafi Da Matar Aure

Jiya mun kawo muku cewa mutane uku ne wasu da ake zargin yan bindiga ne suka bindige har lahira a karamar hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina.

Vanguard ta kuma rahoto cewa an bindige wani mutumin a kafa yayin da yan bindigan sun sace wata mata mai suna Hawau Yusuf mai zaune a Unguwan Makera.

Wani mazaunin garin, Marwan Zayyana, wanda ya tabbatarwa Vanguard lamarin, ya ce maharan sun kai hari garin ne misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin, a kan babura, suka rika cin karansu ba babbaka har 4.30 a garin.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 85, Buhari ya ce lokacin ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya yi

Marwan ya bada sunan wadanda aka kashe din kamar har; Aminu Abdulwahab, Musa Abubakar da Sadiq Lawal.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel