Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kai Wa Yan Sanda Hari, Ana Fargabar Wasu Sun Mutu

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kai Wa Yan Sanda Hari, Ana Fargabar Wasu Sun Mutu

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari shingen yan sanda a Enugu sun halaka jami'ai biyu da wasu mutane
  • Majiyoyi daga babban birnin jihar ta Enugu sun tabbatar da afkuwar lamarin suna mai cewa abin ya faru ne misalin karfe 9.10 na safe a Gariki MTD
  • An nemi ji ta bakin kakakin yan sandan Jihar Enugu, Daniel Ndukwe amma bai gasgata ko karyata rahoton ba, ya ce yana cikin taro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Enugu - Mutane na cikin fargaba a babban birnin jihar Enugu a yayin da wasu yan bindiga suka kai hari shingen binciken yan sanda suka kashe biyu cikinsu da wasu.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da safe a Gariki, MTD a karamar hukumar Enugu South a babban birnin jihar kamar yadda The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai sabon kazamin hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace dandazon mutane

Taswirar Jihar Enugu.
Yan Bindiga Sun Kai Wa Yan Sanda Hari, Ana Fargabar Wasu Sun Mutu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin hada wannan rahoton, majiyoyi sun shaida wa wakilan Punch cewa ana nan ana harbe-harbe a iska a yayin da mutane ke tserewa don neman mafaka.

Sakon text da aka tura wa wakilin majiyar Legit.ng ta ce:

"Ana harbe-harbe a Gariki, MTD kuma an kashe yan sanda biyu da wasu mutanen".

An rahoto cewa yan bindigan sun kai hari shingen yan sandan ne misalin karfe 9.30 na safe.

Babu tabbas ko bata garin ne suka kai hari ofishin yan sanda da ke MTD wanda ba shi da nisa daga shingen yan sandan.

Da aka tuntube shi game da labarin, mai magana da yawun yan sanda na Jihar, Daniel Ndukwe, bai gasgata ko karyata afkuwar lamarin ba.

"Yi hakuri, ina cikin taro ne yanzu," ya ce a cikin sakon text.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.

Asali: Legit.ng

Online view pixel