Katsina: Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Kashe Mutum 3, Sun Tafi Da Matar Aure

Katsina: Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Kashe Mutum 3, Sun Tafi Da Matar Aure

  • Yan bindiga sun hallaka a kalla mutane uku sun kuma raunta wani tare da sace matar aure a harin da suka kai kauyen Katsina
  • Wani mazaunin garin da ya tabbatar da harin, Marwan Zayyana, ya ce maharan sun shafe kimanin mintuna 30 suna adabar mutane
  • Zayyana ya ce miyagun yan bindigan ba su samu damar yi wa mutane fashi ba da sace kayan abinci saboda daga bisani matasan garin sun taso musu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Katsina - A kalla mutane uku ne wasu da ake zargin yan bindiga ne suka bindige har lahira a karamar hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina.

Vanguard ta kuma rahoto cewa an bindige wani mutumin a kafa yayin da yan bindigan sun sace wata mata mai suna Hawau Yusuf mai zaune a Unguwan Makera.

Kara karanta wannan

An kashe akalla mutum 16 a sabon harin da aka kai jihar Benue

Taswirar Jihar Katsina.
Katsina: Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace Matar Aure. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin garin, Marwan Zayyana, wanda ya tabbatarwa Vanguard lamarin, ya ce maharan sun kai hari garin ne misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin, a kan babura, suka rika cin karansu ba babbaka har 4.30 a garin.

Marwan ya bada sunan wadanda aka kashe din kamar har; Aminu Abdulwahab, Musa Abubakar da Sadiq Lawal.

Yayin da Sadiq Lawal an kashe shi ni cikin gidansa a Unguwan Tsugune, Abubakar an kashe shi ne a gaban gidansa a Unguwan Jageme. Na uku shi kuma an kashe shi ne a gonarsa yayin da ya ke tserewa daga maharan.

"A baya-bayan nan ana yawan kawo mana hari. Mako daya da wuce, yan bindiga sun kawo mana hari misalin karfe 2.30 suka sace mutum shida. Har yanzu suna hannunsu a daji.
"A ranar Lahadi ma, an sace wani matashi har yanzu ba a sako shi ba. Jiya, Litinin tsakanin karfe 4-4.30, bata garin sun kawo hari kuma sun kashe mutum uku.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 85, Buhari ya ce lokacin ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya yi

"Bayan mutum ukun da suka kashe, ba a basu damar sun yi sata ba domin matasan garin sunyi kokari sun fattake su," in ji Marwan.

Martanin yan sanda

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya ce bai riga ya samu rahoton ba, ya yi alkawarin zai bada bayani da zarar ya samu rahoton.

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

A wani rahoton, Yan sanda a Abuja a safiyar ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022, sun ceto mutane hudu daga mabuyar masu garkuwa a Dutsen Dudu a unguwar Kuje sun kuma lalata maboyar yan ta'addan.

Rundunar yan sandan ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel