Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci, ya aika sunayen majalisa don tabbatar da su
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake sabbin nade-nade masu muhimmanci a yau Laraba, 22 ga watan Yuni
- Buhari ya aikawa majalisar dattawa sunan Mohammed Bello Shehu don tabbatar da shi a matsayin shugaban Hukumar RMAFC
- Ya kuma nemi majalisa ta tabbatar da nadin Joe Aniku Michael Ohiani Babban Darakta/ Shugaban Hukumar ICRC
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dattawa ta tantance tare da tabbatar da Mohammed Bello Shehu a matsayin shugaban Hukumar Tatattarawa da Rarraba Kudin Shigar Gwamnati (RMAFC).
Wannan bukata ta Buhari na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike majalisar wacce shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanto a yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 22 ga watan Yuni, jaridar Vanguard ta rahoto.
Wasikar ta ce:
“Kamar yadda yake a tanadi na sashi 154(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ina mai gabatar maku da sunan Mohammed Bello Shehu don majalisar dattawa ta tabbatar da shi a matsayin shugaban Hukumar Tatattarawa da Rarraba Kudin Shigar Gwamnati (RMAFC).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Takardunsa na manne a nan.
“Ina fatan cewa majalisar dattawa za ta yi nazari tare da tabbatar da wanda aka nada kamar yadda ta saba."
Hakazalika, shugaban majalisar dattawan ya gabatar da bukatar Buhari na neman a tabbatar da nadin Joe Aniku Michael Ohiani Babban Darakta/ Shugaban Hukumar ICRC.
Ya kuma gabatar da bukatar shugaban kasa na tabbatar da nadin Umar Yahaya a matsayin mataimakin shugaban hukumar kudaden da babu masu shi.
Ana sanya ran mutanen za su gurfana a gaban kwamitocin da suka dace domin tantance su, jaridar Independent ta rahoto.
An ba kwamitocin makonni biyu su kawo rahotonsu a zauren majalisar dattawan.
Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani
A wani labarin, Tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce ya so ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake zabar Rotimi Amaechi a matsayin ministan sufuri.
Daily Trust ta rahoto cewa Sani ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, a yayin hira da gidan talbijin na Channels.
Buhari dai ya aika da sunayen mutane bakwai zuwa majalisar dattawa domin a maye gurbinsu da ministocin da suka yi murabus don neman mukaman siyasa.
Asali: Legit.ng