Babbar magana: Majisar dokokin jihar Arewa ta tsige kakakinta, da wasu 3 saboda dalilai

Babbar magana: Majisar dokokin jihar Arewa ta tsige kakakinta, da wasu 3 saboda dalilai

  • Majalisa dokokin jihar Kogi ta tsige wasu manyan 'yan majalisa daga mukamansu saboda zargin rashin da'a
  • Wannan na zuwa ne yayin da majalisar ta kira tarion gaggawa don sanar da tsige manyan jam'an na majalisa
  • Daga cikinsu, akwai kakakin majalisar dungurungum, wanda tuni aka bayyana wanda zai maye gurbinsa

Kogi - An tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kogi Rt Hon Ahmed Muhammed da wasu manyan jami'an majalisar dokokin jihar guda uku.

Majalisar ta dauki wannan mataki mai tsauri na ladabtarwa ne yayin wani taron gaggawa da aka yi a ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni, inji rahoton Punch.

An tsige kakakin majalisar Kogi da jami;ai uku
Babbar magana: Majisar dokokin Kogi ta tsige kakakinta saboda dalilai | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Manyan 'yan majalisar uku da aka kora daga majalisar sun hada da shugaban masu rinjaye, Bello Hassan Balogun, mataimakin shugaban masu rinjaye, Idris Ndako, da kuma Hon Edoko Moses Ododo.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku: 'Zunuban' Wike, Dalilan Da Yasa Aka Zabi Okowa, Majiya Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Wannan matakin dai ya zo ne a matsayin martani ga zargin rashin da'a da kuma amfani da ofishi ba bisa ka'ida ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani kudiri na gaggawa wanda mamba mai wakiltar mazabar Dekina/Okura, Enema Paul ya karanta, ‘yan majalisa 17 ne suka rattaba hannu a kan tsige Hon Ahmed Mohammed da kuma dakatar da wasu manyan jami’ai uku a majalisar.

Majalisar ta kuma bayyana Alfa Momoh Rabiu, dan majalisa mai wakiltar Ankpa II a matsayin wanda zai maye gurbin kakakin majalisar da aka tsige.

Kafin aiwatar da tsigewar, Leadership ta ce an dasa tarin jami’an tsaro a harabar majalisar da suka hada da ‘yan sanda, da jami’an tsaro na hukumar NSCDC, da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

‘Yan majalisar 17 cikin 25 ne suka halarci zaman.

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Kara karanta wannan

Yan majalisa na shirin tsige mataimakin gwamna bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

A wani labarin, a jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce masu daukar doka a hannunsu, rike makamai ba bisa ka’ida ba da kuma cin gajiyar rashin tsoro za su fuskanci hukunci mai tsauri daga gareshi.

Ya yi jawabi ne a Wudil, Kano, a wajen bikin faretin yaye dalibai na kwas na hudu na makarantar ‘yan sanda ta Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da nuna rashin amincewa da aikata munanan laifuka, inda ya bukaci ‘yan sanda da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukansu na dakile 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel