Bidiyo: Mai Kwashe Shara Dake Karbar N50 Kudin Aikinsa Ya Gigice Bayan An Bashi Kyautar N50k

Bidiyo: Mai Kwashe Shara Dake Karbar N50 Kudin Aikinsa Ya Gigice Bayan An Bashi Kyautar N50k

  • A wani bidiyo da ya yadu, an ga yadda wani mutumi dan Najeriya mai matukar kirki ya bawa wani talaka wanda bai san daga inda yake ba N50,000 da wani ya turo masa
  • Kyautar tazo ne bayan wasu kwanaki da mutumin ya yi wani bidiyon sanda ya hadu gami da ba mutumin da bai sansa ba kyautar N5,000 ya ci abinci
  • 'Yan Najeriyan da ke amfani da shafin TikTok da suka kalli bidiyon sun yi addu'a tare da fatan alkhairi ga wanda ya yi kyautar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani mutum 'dan Najeriya mai matukar kirki mai amfani da @mrsucessguy a shafin TikTok ya sauya rayuwar wani talaka da ya gani gefen titi.

Idan za ku tuna, zuciyar mutumin ta karye ne yayin da ya ga talakan na aikin kwashe shara don samun N50.

Kara karanta wannan

Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori

Mutumin Kirki Ya Gwangwaje Mai Kwashe Shara da N50,000
Bidiyo: Mai Kwashe Shara Dake Karbar N50 Kudin Aikinsa Ya Gigice Bayan An Bashi Kyautar N50k. Hoto daga @mrsuccessguy
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama sun jinjinawa matashin a kan irin tausayi da jin kan da ya nuna.

Ya bawa mutumin N5,000 tare da ce masa ya yi amfani da shi ya cika kundunsa.

Yayin martani ga wani mutum da ya ce ya yi hakan ne don ya nunawa jama'a, ya wallafa sabon bidiyon martani ga mutumin.

A bidiyon, ya bawa talakan kyautar N50,000 tare da ce masa ya je ya canza kayan jikinsa don ya fito tsaf.

@mrsuccessguy ya shaidawa masu tsokaci karkashin bidiyon da ya wallafa da farko ne ya janyo kyautar N50,000 din.

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama'a a karkashin wallafar

sootosooto ya yi martani: "Ka yi kokari 'dan uwa, ina rokonka ka tabbatar ka yi bidiyo duk lokacin da za ka taimaki wani, don ka karfafa mutane su yi abun kwarai."

Kara karanta wannan

Kuri'arku 'yancinku: Sheikh Gumi ya yanki katin zabe, ya ba 'yan Najeriya shawara

Ewa tomilola ta ce: "Ina matukar godiya 'dan uwana na jini, Ubangiji Allah ya albarkace ka."
TikTok Live Delegate ya ce: "Ba za ka ga yalwa a rayuwarka ba? To fa... baba ya yi tsinuwa."
Olamilekan ya ce: "Ubangiji ya cigaba da yi maka albarka."
Islamiyat oluwaseyi ya ce: "Aikin ka na kyau 'dan uwa, Ubangiji ya cigaba da maka albarka."

Hotunan Tsohon Dalibin UNIMAID Yana Tura Kurar Ruwa Don Samun na Abinci, Hoton Kwalin Digirinsa Ya Bayyana

A wani labari na daban, hotunan wani 'dan Najeriya mai digiri sun yadu yana tura kurar ruwa a jihar Taraba. Mutumin da aka gano sunansa Kawu Malami, ya karanci injiniyancin noma da kiwo tare da muhalli a jami'ar Maiduguri Yana da wasu shaidun kammala karatuttuka.

Hotunan sun yadu ne bayan wata budurwa mai amfani da suna @_Hafsat_paki wacce ta hada da hotunan takardun makarantarsa ta wallafa a shafinta.

Kara karanta wannan

Na gazawa mutanena: Gwamnan Ondo ya fashe da kuka wiwi yayin binne wadanda harin coci ya ritsa da su

Daya daga cikin takardun shaidar kammala karatunsa na injiniyanci ya nuna cewa an bashi takardar a ranar 15 ga watan Janairun 2015 daga jami'ar Maiduguri kuma tabbas sunan Kawu ne a kai. Ya samu shaidar digiri mai daraja ta hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel