Hotunan Tsohon Dalibin UNIMAID Yana Tura Kurar Ruwa Don Samun na Abinci, Hoton Kwalin Digirinsa Ya Bayyana

Hotunan Tsohon Dalibin UNIMAID Yana Tura Kurar Ruwa Don Samun na Abinci, Hoton Kwalin Digirinsa Ya Bayyana

  • Wani 'dan Najeriya da ya kammala digirinsa daga jami'ar Maiduguri, Kawu Malami, ya koma tura kurar ruwa tare da siyar da ruwan
  • Kawu wanda ya karanci fannin Injiniyancin noma da kiwo tare da muhalli, ya koma jihar Taraba inda yake kasuwancin ruwa
  • Hotunan shaidar kammala karutunsa sun bayyana inda mutane da yawa suka bayyana cewa sun san shi har da wani da suka zauna daki daya a jami'a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hotunan wani 'dan Najeriya mai digiri sun yadu yana tura kurar ruwa a jihar Taraba. Mutumin da aka gano sunansa Kawu Malami, ya karanci injiniyancin noma da kiwo tare da muhalli a jami'ar Maiduguri

Yana da wasu shaidun kammala karatuttuka. Hotunan sun yadu ne bayan wata budurwa mai amfani da suna @_Hafsat_paki wacce ta hada da hotunan takardun makarantarsa ta wallafa a shafinta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan jinya a Landan, an sallami tsohon shugaban Najeriya a asibiti

Injiniya Kawu Malami Dake Turin Kurar Ruwa
Hotunan Tsohon Dalibin UNIMAID Yana Tura Kurar Ruwa Don Samun na Abinci, Hoton Kwalin Digirinsa Ya Bayyana. Hoto daga @_hafsat_paki
Asali: Twitter

Daya daga cikin takardun shaidar kammala karatunsa na injiniyanci ya nuna cewa an bashi takardar a ranar 15 ga watan Janairun 2015 daga jami'ar Maiduguri kuma tabbas sunan Kawu ne a kai. Ya samu shaidar digiri mai daraja ta hudu.

Hakazalika, Tsangayar Malamai ta kasa dake Kaduna ta bai wa Kawu shaidar kammala karatu a shekarar 2001. Kawu yana da shaidar karatun nazarin na'ura mai kwakwalwa wanda jami'ar Maiduguri ta bashi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Siyar da ruwa domin neman abinci

A yayin wallafa hotunan, @_hafsat_paki ta rubuta: "Wannan shi ne Kawu Malami, mai digiri daga jami'ar Maiduguri. Malami ya karanci fannin injiniyancin noma da kiwo tare da muhalli amma yanzu siyar da ruwa yake yi a Taraba domin neman na kai."

Wani yayi martani inda ya tabbatar da ikirarinta tare da bayyana cewa wannan tabbas sun zauna daki daya da shi yayin da suke makaranta yayin da wani yace ya bar aikinsa a Bauchi inda ya koma Taraba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Najeriya ta kuduri kawar da amfani da kananzir nan da 2030

'Yan Najeriya sun yi martani a kan wallafar

@SlyyoldeWears yace: "Wannan dakinmu daya!"
@Samuel49273839 yayi tsokaci da: "Haka duniya ta mayar da 'yan Najeriya. Wannan ne yasa zaka ga sauran yankunan suna fatan a samu shugaba nagari a kasar nan."
@AU_Marte "Halin da yake ciki ya kazanta ga mai digiri gaskiya. Amma idan aka yi tunani, mutum nawa ne ke cikin irin wannan halin ko kuma fiye da hakan. Na jinjina masa ta yadda bai zauna babu abun yi ba yana jiran aiki daga gwamnati."
@humanitarian_w yace: "Wannan mutumin da ka gani daga karamar hukumar mu yake a jihar Bauchi kuma yana aiki da ma'aikatar ilimi har ya kai mataki na 12, ya bar aikinsa inda ya koma Taraba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel