An damke mai hadawa yan Boko Haram Bam a Taraba, an gano bama-bamai 27

An damke mai hadawa yan Boko Haram Bam a Taraba, an gano bama-bamai 27

  • An damke daya daga cikin masu kai harin bam mashaya a jihar Taraba, Arewa maso gabashin Najeriya
  • Dan ta'addan ya bayyana cewa shi dan kungiyar yan ta'addan Boko Haram ne masu tada kayar baya
  • An damkesa da bama-bamai ashirin da bakwai da kuma sinadaren hada bama-bamai da dama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jalingo - Hukumar yan sandan jihar Taraba ta damke wani da ake zargin yana hada Bam kuma dan kungiyar Boko Haram wanda ya kai harin bam 3 a jihar a shekarar nan.

An damke mutumin ne a gidansa da yake hada bama-bamai a garin Tella, karamar hukumar Gassol ta jihar, rahoton ChannelsTV.

An damkeshi da makamai, harsasai, bama-bamai da kayan hada bama-bamai kan laifin bam din da aka saka a mashaya dake Nukkai, Jalingo.

TNP Jalingo
An damke mai hadawa yan Boko Haram Bam a Taraba, an gano bama-bamai 27 Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Bincike ya nuna dukiyar Attajirai 2 za ta iya fito da mutum miliyan 63 daga talauci

Kwamishanan yan sandan jihar, Abimbola Sokoya, ya sanar da hakan wa manema labarai a hedkwatar hukumar dake Jalingo, riwayar Punch.

Sokoya yace:

"Mutumin ya yi kokarin kashe wani Usman Yaki dan garin Gunduma kuma aka sanar da yan sanda. Yan bijilanti sun taimaka wajen damkeshi."
"Yayin bincike, mutumin ya tabbatar mana cewa shi dan Boko Haram ne kuma sun kai hare-hare Neja, Kogi, da Taraba."
"Mun gano harsasan 7.6mm guda 198, harsasan assault live 558, karamar bindiga 1, ruwan acid na Sodium Azide."
"Sauran kayayyakin sun hada da robobin Kermi Acid 8, bama-baman gargajiya 27, leta, dss."

Yayin hira da yan jarida, wanda aka damke ya bayyana cewa akwai abokan aikinsa takwas.

kwamishanan yan sanda ya bayyana cewa ana kokarin damke sauran abokansa masu suna Abubakar Lawal da Abdullahi Garba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel