Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook

Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook

  • Kotu ta ɗaure wani mutumi na tsawon wata biyu a gidan Gayaran hali bayan kama shi da laifin yaɗa ƙarya kan COVID19 a Facebook
  • Mutumin mai suna, Habibu Rabiu, ya yi wani rubuta inda ya ankarar da mutane cewa rasa rayuka na ƙaruwa a Kogi sanadiyyar zazzaɓi
  • Wanda ake zargin zai biya N5,000 kamar yadda doka ta tanada sannan ya shafe hukuncin Kotu a gidan yari

Kogi - Wani Mutumi, Habibu Rabiu, zai yi zaman gidan gyaran hali na tsawon wata biyu saboda watsa bayanan ƙarya a shafinsa na dandalin Facebook, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kama Rabiu kuma ta gurfanar da shi a gaban Kotu kan wani rubutu mai taken, "Yawan mace-macen da ake samu sanadiyyar zazzaɓi a jihar Kogi abun damuwa ne."

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Jaruma Hadiza Gabon da aka gurfanar a Kotun Musulunci

Alamar manhajar Facebook.
Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kotu ta ba da belin shi bayan gurfanar da shi kan tuhumar, "Yaɗa bayanan ƙarya da ka iya tada hankula da jawo jinya tsakanin al'umma."

Rahoto ya nuna cewa Rabiu ya yi rubutun a lokacin dokar kulle sakamakon barkewar Annobar Korona Biros a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda zaman Kotu ya kaya

Yayin zaman Kotu na ranar Talata, lauya mai gabatar za ƙara, Mista M. A. Abaji, yace abin da wanda ake ƙara ya aikata ya saɓa wa sashi na 393 a kundin Fenal Kod a jihar Kogi.

Rubutun nasa a cewar lauyan ya jefa mutane cikin tsoro da kuma tunzura al'umma su fusata da gwamnatin jihar Kogi. Ya kuma yaɗa ƙaryar yawaitar rasa rai yayin da ake fama da Annoba a 2020.

Lauyan ya ƙara kafa hujja da jami'in da aka gayyata ya bada shaida kan ikirarin Rabiu, wanda ya bayyana wa Kotun cewa lokacin da wanda ake zargi ya yi rubutun, alkaluman rasa rayuka a Kogi na nan yadda suke.

Kara karanta wannan

2023: PDP na tsaka da kokarin zaɓo mataimakin Atiku, Sanata mai ci ya sauya sheƙa zuwa APC a hukumance

A ɓangaren lauyan da ke kare wanda ake zargi, E .A. Iwu, ya ce Rabiu ya yi haka a cikin yanayin ɗimuwa, bayan yar uwarsa wacce ke fama da zazzaɓin cizon sauro ta rasa rayuwarta.

Wane hukunci Kotu ta yanke?

Alƙalin Kotun mai shari'a A.A. Agatha, ta yanke wa wanda ake ƙara hukuncin zaman gidan yari na wata biyu ba tare da zaɓin tara ba a matsayin kari kan biyan N5,000 da doka ta tanada.

Bayanai sun nuna cewa mutumin da ake zargin ya biya kuɗin kafin jami'ai su tasa shi zuwa gidan Yari.

A wani labarin kuma Daga karshe, Atiku Abubakar ya zaɓi wanda yake so ya zama mataimakinsa a 2023

Bayan dogon lokaci ana kace nace, wasu bayanai sun tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya zaɓi wanda ya ke so ya zama abokin takararsa.

Jam'iyyar PDP ta tsinci kanta cikin ƙaƙanikayi game da wanda zai zama mataimaki, sai dai Gwamna Wike da Okowa ne a sahun gaba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

Asali: Legit.ng

Online view pixel