Dirama a Kotu: Ba kai ne mahaifin ɗan da na haifa ba, Wata mace yar sanda ta faɗawa mijinta a Kotu

Dirama a Kotu: Ba kai ne mahaifin ɗan da na haifa ba, Wata mace yar sanda ta faɗawa mijinta a Kotu

  • Dirama ta ɓalle a Kotu yayin da miji ya kai ƙarar matarsa kan ɗan da suka haifa amma ta gaya wa Kotu cewa ba shi ne uban ɗan ba
  • Magidancin ya nemi Kotu ta dawo masa da ɗansa kuma ta raba auren da ke tsakaninsu saboda matar ta guje shi
  • Sai dai matar wacce take jami'ar hukumar yan sanda ta faɗa wa Kotu duk abin da ya faru tun da farko

Ekiti - Wata Kotun Kostumare da ke zamanta a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, ta rushe auren da ke tsakanin Mista Ige Iyiola da Misis Ojo Funmilayo.

Daily Trust ta ruwaito cewa Magidanci ya kai ƙarar matar ta sa gaban Kotu ne domin ta ba shi damar shiga lamurran ɗa ɗaya da suka haifa kuma ya buƙaci kotun ta raba auren.

Kara karanta wannan

Dirama a Kotu: Ɗan sanda ya faɗi yadda wani Mutumi ke saduwa da 'ya'yansa mata biyu ba kunya

Sakin aure a Kotu.
Dirama a Kotu: Ba kai ne mahaifin ɗan da na haifa ba, Wata mace yar sanda ta faɗawa mijinta a Kotu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Amma wacce ake ƙara Misis Funmilayo, jami'ar hukumar yan sandan Najeriya, ta musanta haifar ɗa tare da Magidancin, Iyiola.

Ta faɗa wa Kotun cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na samu ciki har sau huɗu tare da shi, amma dukkan su zuɓe wa suka yi ta sanadinsa."
"Lokaci na ƙarshe da na samu ciki da shi kuma ya zube shi ne a farkon shekarar 2015, na gudu na bar masa gidansa kuma na samu ciki na haihu a watan Satumba, 2016."
"Mahaifin ɗana shi ne Debo Oluranti, kuma na haɗu da shi ne bayan na bar gidan wanda ya kawo ƙara ta."

Bayan haka matar ta amince da cewa a gwada kwayoyin halittar yaron don tabbatar da mahaifinsa na gaskiya.

Wane mataki Kotun ta ɗauƙa?

Alƙalin Kotun mai shari'a, F. O. Oyeleye, ta gano cewa ɓangarorin biyu sun rabu da juna tsawon shekara Bakwai kuma ba su da sha'awar sake komawa inuwa ɗaya.

Kara karanta wannan

Dirama yayin da Jami'an tsaro mata biyu suka buɗa, suka ba hammata iska a filin taron APC

Saboda haka ta ba da umarnin cewa ta rushe igiyoyin auren, inda ta ƙara da cewa kowanen su na da ikon ɗaukaka ƙara nan da kwanaki 30.

A wani labarin na daban kuma Wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya zabi wanda zai zama mataimakinsa a 2023

Yayin da manyan jam'iyyu ke ta faɗi tashin neman mataimaki, Farfesa Umeadi, ya kawo karshen kace-nace a jam'iyyar APGA.

Ɗan takarar da jam'iyyarsa sun amince Kwamaret Muhammed Koli ya zama mataimaki yayin zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel