Abun Kallo ya samu: Bidiyon yadda wasu Jami'an tsaro mata suka damabace a filin taron APC

Abun Kallo ya samu: Bidiyon yadda wasu Jami'an tsaro mata suka damabace a filin taron APC

  • Wasu jami'an tsaro mata su biyu sun buɗa a filin taron APC, sun bai wa hammata iska har sai da aka shiga tsakanin su
  • Wani bidiyo ya bayyana yadda jami'ar hukumar yan sanda da kuma yar uwarta ta hukumar Cibil Defence suka dambace a Eagle Square
  • Yanzu haka dai ana cigaba da ƙidaya kuri'u bayan kammala ƙada kuri'u, Bola Tinubu ke kan gaba tun da farko

Abuja - Wasu jami'an tsaro mata daga hukumar yan sanda da kuma hukumar Cibil Defence NSCDC sun bai wa hammata iska a wurin taron APC da ke gudana a Abuja.

A wani Bidiyo da ya watsu a kafar sada zumunta ya nuna yadda jami'an mata suka dambace bayan wani ɗan saɓani ya shiga tsakanin su yayin da suke aiki a Eagle Square.

Kara karanta wannan

NNPP 2023: Da zaran na zama gwamnan Kano masu cin hanci sun shiga uku, Abba Gida-Gida

Filin taron jam'iyyar APC.
Abun Kallo ya samu: Bidiyon yadda wasu Jami'an tsaro mata suka damabace a filin taron APC Hoto: @OfficialAPCNigeria
Asali: UGC

Sauran jami'an tsaro da ke kusa da wurin sun yi gaggawar shiga tsakani domin raba su amma jami'ar NSCDC ɗin na ƙara shigewa

Kalli Bidiyon anan:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yau Laraba, rana ta uku tun bayan fara harkokin zaɓen fidda gwanin APC, bayanai sun tabbatar da cewa an kammala zaɓe kuma yanzu haka ana aikin ƙidaya kuri'u.

Tinubu na kan gaba a Akwatin farko

Tun kafin fara taron, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci Deleget su natsu su zaɓi ɗan takara mai kishin Najeriya da zai ɗora daga inda gwamnatin zata tsaya.

A halin yanzun bayan kammala zaɓe, alamu sun nuna jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shi ke jan ragama da farko farko, kuma an kammala da akwatin farko.

Tinubu ya samu goyon bayan a filin taron lokacin da wasu yan takara suka sanar da janye wa kuma suka umarci magoya bayansu da su zaɓi Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

2023: Mace Guda Da Ke Takarar Shugaban Kasa a APC Ta Janye Wa Tinubu, Ta Bayyana Dalili

A wani labarin na daban kuma Abba Gida Gida ya ce idan ya zama gwamnan Kano a 2023 zai hana masu cin hanci da rashawa sakat

Ɗan takarar kuma surukin Sanata Kwankwaso, ya ce duk lalacewar da Kano ta yi idan ya zama gwamna komai zai zama tarihi.

Abba ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga dubbannin magoya bayansa da suka taru a cibiyar Abacha Youth Centre a Kano domin tabbatar masa da takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel