Hotuna: 'Dan Najeriya ya Tsinta Abarba a Teku Dauke da Hoton Saurayi da Budurwa an Dinke

Hotuna: 'Dan Najeriya ya Tsinta Abarba a Teku Dauke da Hoton Saurayi da Budurwa an Dinke

  • Wani 'dan Najeriya ya tada kura a yanar gizo bayan ya wallafa hoton wani mutum da wata mata daure jikin abarba da ya tsinta a gefen teku
  • Mutumin da ya cika da tsananin mamaki ya yi hasashen ta yuwu wani kulunboto ne a aka yi don hada soyayya ta hanyar amfani da sihiri
  • Mutumin ya ce zai tafi da sihirin gida tare da kwance sammun bayan tsawon kwanaki uku don ya shiga tsakanin masoyan biyu

Wani mai amfani da shafin Twitter da @TheOnlyCleverly ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar bayan ya wallafa wani kulunboton sihiri da aka yi don hada wasu masoya inda ya gani a gefen wata teku.

Sihirin hada masoyan shi ne hotuna biyu na mace da namiji da aka daure cikin wata abarba, wanda mutane da dama sun yi imani an yi ne don a haddasa matsananciyar kauna mai dorewa tsakanin masoyan biyu.

Hotuna: 'Dan Najeriya ya Tsinta Abarba a Teku Dauke da Hoton Saurayi da Budurwa an Dinke
Hotuna: 'Dan Najeriya ya Tsinta Abarba a Teku Dauke da Hoton Saurayi da Budurwa an Dinke. Hoto daga @TheOnlyCleverly
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, zai kwance abarbar na kwanaki uku sannan ya sake daurewa na tsawon kwanaki uku don ya hada masoyan rikici.

Me Mawallafin yace?

Tsokacin mawallafin:

"Yanzu zan tafi da shi gida in kwance na tsawon kwanaki uku sannan in sake daurewa bayan kwanaki uku. Za su yi fada na kwanaki uku sannan su so juna na kwana uku, hakan yafi komai dadi."

Jama'a sun yi martani

Tsokacin jama'a:

@ALFitZ0 ya ce: "Idan ka sake daurewa, za ka bukaci wani ya kwance bayan mako biyu, saboda ba za ka san illar da zai maka ba."
@Ejiro_OS ta ce: "Ba za ka bar mutumin da ya yi sihirin ya dan mora kadan ba ma. Daga gani sabon sihiri ne tunda ga abarbar nan har yanzu sabuwa ce. Ka maida wa mutum abun shi ka daure mana."

@Logg2media ya ce: "Kai cire hoton saurayin a wurin sannan ka daure sihirin. Yadda budurwar za ta ji tana kaunar kanta sosai."
@MiaturSanjay ya ce: "Wannan wani aiki ne da ya same ka. Kawai ka bude wani wurin hada soyayya, yadda za ka dinga karbar kudi ita kuma wannan yarinyar sai ta dinga sallamar kwastomominka. Kawai ka nemi hotunan kwastomominka ka sa a jikin wannan abarbar tare da yarinyar, ka daure na wasu awanni.
"Kana iya samun kwastomomi hudu zuwa biyar a rana."

Asali: Legit.ng

Online view pixel