Kano: Hisbah ta kama wani mutumi da ya 'gina gida' da Shafukan Alkur'ani

Kano: Hisbah ta kama wani mutumi da ya 'gina gida' da Shafukan Alkur'ani

  • Hukumar Hisbah mai kokarin tabbatar da Shari'ar Musulunci a Kano ta kama wani mutumi bisa zargin gina gida da shafukan Alkur'ani
  • Mataimakin kwamandan Hisbah, Ustaz Usaini Usman, ya ce dakaru sun kamo mutumin tare da malamin da ya ba shi fatawa
  • A cewarsa, me gidan ya faɗa musu cewa ya yi haka ne da nufin neman tsari daga sharri kowane iri

Kano - Rundunar Hisbah da ke kokarin tabbatar da bin dokokin Musulunci a Kano ta ce ta cafke wasu mutane uku da take zargin sun yi amfani da shafukan littafi mai tsarki wajen yin gini.

BBC Hausa ta rahoto cewa waɗan da ake zargin sun yi amfani da wasu shafukan Alƙur'ani mai tsarki ne wajen gina gida a Anguwar Gaida ta jihar Kano.

Hukumar Hisbah a Kano.
Kano: Hisbah ta kama wani mutumi da ya 'gina gida' da Shafukan Alkur'ani Hoto: bbchausa.com
Asali: UGC

Mataimakin rundunar yan sandan Musuluncin mai kula da sashin ayyuka na musamman, Ustaz Usaini Usman Ceɗiyar Ƴan Kuɗa, ya shaida wa manema labari cewa sun kama me gidan da Malamin da ya ba shi fatawar hakan.

Kara karanta wannan

Firgici: An cafle mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari

Ya ƙara da cewa yayin da dakarun Hisbah suka dira wurin, sun ga an kwaɓa Simintin gini da irin waɗan nan takardu na wani sashin Littafin Allah mai tsarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane sun rushe gidan

A jawabinsa da wakilin jaridar, Ustaz Usaini ya ce tuni ma'aikatan da ke aikin ginin da wasu mazauna anguwan suka rushe gidan baki ɗaya.

Ya ce:

"Mun kama me gidan da Malamin da ya ba shi fatawar yin haka. Mutumin ya faɗa mana yana haka ne don samun tsaro, shi kuma Malamin ya ce ya amince a yi haka ne saboda me gidan ɗalibinsa ne."
"Ma'aikatan da ke aikin akasarin su basu san me aka yi ba da farko, da wasu mutane sun rushe gidan, kuma lokacin da jami'ai suka isa sun ga ana kwaɓa yashi da takardun."

Wane mataki Hisbah zata ɗauka?

Kara karanta wannan

Dirama a Kotu: Ɗan sanda ya faɗi yadda wani Mutumi ke saduwa da 'ya'yansa mata biyu ba kunya

Mataimakin shugaban ya ce a halin yanzun suna cigaba da gudanar da bincike kuma da izinin Allah da zaran sun gama zasu miƙa lamarin ga hukuma ta gaba don ɗaukar mataki.

A wani labarin kuma Ɗan Sarauniya ya tura sakon neman Afuwa ga gwamna Ganduje kan rubutunsa na Facebook

Tsohon kwamishinan ayyuka da tsare-tsare na jihar Kano, Muaz Magaji, ya aike da sakon neman yaf iy a ga gwamna Ganduje.

Injiniya Magaji, wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya ya samu saɓani da gwamnan ne bayan yin wani rubutu a Facebook da ya taɓa kimar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel