Firgici: An cafke mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari

Firgici: An cafke mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke wani mutumin da ya tada hankalin jama'a ba gaira ba dalili a jihar Ogun
  • Mutumin dai ya yada wani sakon murya ne da ke ikrarin 'yan ta'addan Boko Haram sun shiga Ogun, lamarin ya haifar da firgici
  • Da aka kwamushe shi, ya bayyana cewa ya yi hakan ne don tsorata jama'a da tada hankalinsu ne kawai ba komai ba

Jihar Ogun - Daily Trust ta rahoto cewa, rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Wakilu Ogundairo bisa zarginsa da tayar da hankalin jama'a da cewa kungiyar Boko Haram ta farmaki garin Imosan-Ijebu da ke karamar hukumar Ijebu-Ode a jihar.

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce wanda ake zargin ya yi ikrari a sakon murya ta Whatsapp da aka yada ga jama’a kan wannan lamari.

Kara karanta wannan

Kuma a Najeriya: Fasto ya ba da tarihin cocinsa, ya ce tun 1999 ba a dauke musu wuta ba

Wani ya tada hankali da sakon Boko Haram sun shigo Ogun
Firgici: An cafle mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari | Hoto: vamguardngr.com
Asali: UGC

Ogundairo ya yi ikirarin cewa maharan na dauke da makamai, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin da kuma kewayensa.

Kakakin ‘yan sandan ya ce mutane suna kiran lambar gaggawar ta rundunar suna nuna damuwa kan lafiyar ‘yan uwansu a Ijebu-Ode da kuma jihar baki daya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da 'yan sanda suka gano

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya umurci jami’in ‘yan sandan reshen Obalende, da ya shiga yankin domin gano sahihancin sakon muryar da ke ta yawo a WhatsApp, inji rahoton Premium Times.

Oyeyemi ya ce da aka gudanar da bincike, an gano cewa, mutanen da ke wurin ma’aikatan gona ne daga jihar Benue da ke gudanar da sana’arsu ta halal ba tare da wani tashin hankali ba.

Ya ce "binciken fasaha" na 'yan sanda ya kai ga kama wanda ake zargi da yada labarin na bogi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsageru sun sace mai daukar hoton gidan gwamnatin jiha, suna neman N50m

Ya ce da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya nadi muryar ne don ya tsoratar da mutane.

Rundunar ‘yan sandan ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

'Yan bindiga sun harbe mai shayi, direba da 'yan kasuwa a jihar Ondo

A wani labarin na daban, wasu ‘yan bindiga da ke barna a kan babura sun harbe wasu mutane hudu da suka hada da masu sayar da shayi da wani direba da kuma ‘yan kasuwar gefen hanya har lahira.

Kisan ya faru ne a kusa da Sabo da Igba a cikin garin Ondo a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Wata majiya ta ce wasu ’yan kungiyar asiri ne suka kai hari kan wata kungiyar asirin, rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel