Saboda N100 Kacal, Direba Ya Ciro Wuka Ya Caka Wa Fasinjansa Yayin Da Rigima Ya Kaure Tsakaninsu, Dan Sanda

Saboda N100 Kacal, Direba Ya Ciro Wuka Ya Caka Wa Fasinjansa Yayin Da Rigima Ya Kaure Tsakaninsu, Dan Sanda

  • An gurfanar da wani direban motar haya a gaban kotun Majistare a Kaduna kan zarginsa da caka wa fasinja wuƙa
  • Mai gabatar da kara a kotu, Sufeta Leo Chidi ya ce direban ake zargi ya daba wa fasinjan wukan ne kan N100 da suke rikici a kai
  • Direban da aka yi ƙarar a kotu, mazaunin Gonin-Gora a Kaduna ya musanta zargin da aka masa kuma Alkali ya bada belinsa kan N200,000 ya dage cigaba da sharia

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - An gurfanar da wani direban mota, Silas Vincent, dan shekara 38 a gaban kotun Majistare da ke Kaduna kan zarginsa da daɓa wa fasinjansa wuka yayin musu kan kudin mota.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN ta rahoto cewa yan sanda sun gurfanar da mutumin mazaunin Gonin-Gora a Kaduna kan laifin kai hari da yin mummunan rauni.

Kara karanta wannan

Harin cocin Ondo: Tinubu ya bayar da tallafin miliyan N75, ya yi kira ga inganta tsaro

An Gurfanar da Direba a Kotun Kan Zarginsa da Daɓa Wa Fasinja Wuƙa Kan N100
An Gurfanar da Direba a Kotun Kan Zarginsa da Daɓa Wa Fasinja Wuƙa Kan N100. @daily_trust.
Asali: UGC

Mai gabatar da kara, Sufeta Chidi Leo, ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a Stadium Round About, Ahmadu Bello Way Kaduna a ranar 28 ga watan Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Leo, rikici ya barke tsakanin wanda aka yi ƙarar da wani Emmanuel Isaac kan kudin mota N100.

Mai gabatar da karar ya ce yayin fadar, wanda aka yi ƙarar ya ciro wuka daga aljihunsa ya caka wa wanda ya yi ƙarar a kafadarsa da bayansa.

Leo ya ƙara da cewa an garzaya da wanda ya yi ƙarar zuwa wani asibiti da ke kusa inda aka yi masa magani.

Mai gabatar da ƙarar ya ce laifin ya saba da sashi na 173 da 284 na Penal Code na Jihar Kaduna ta shekarar 2017.

Martanin wanda aka yi ƙarar

Kara karanta wannan

Samun wuri: 'Yan ta'addan IPOB sun banka wa motar siminti wuta a jihar Kudunci

Bayan karanto masa tuhumar, wanda aka yi ƙarar ya musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel ya bada belin wanda ake zargin kan kudi N200,000 tare da mutum biyu wanda za su tsaya masa.

Ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 28 ga watan Yuni kamar yadda NAN ta rahoto.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164