Kai karamin kwaro ne: Zulum ya mayarwa Jajari martani mai zafi

Kai karamin kwaro ne: Zulum ya mayarwa Jajari martani mai zafi

  • Biyo bayan zargin gwamnatin Zulum da baiwa yan'uwa da abokan arziki kwangila maimakon yan kwangilan gaske, Gwamna Zulum ya yi raddi
  • Zulum ya ce kada jama'a su saurari babatun Jajari saboda ko a jihar Borno babu wanda ya sanda zamansa
  • Mohammed Jajari yace babu wani aikin kirki da Gwamna Babagana Zulum yayi, kawai duk karya ce

Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi kira da masoyansa suyi watsi kalaman dan takaran gwamnan jihar na jam'iyyar adawa ta PDP, Mohammed Ali Jajeri.

Mai magana da yawun Gwamna Zulum, Isa Gusau, ya bayyana cewa Gwamna Zulum ko kadan ba zai bata lokaci wajen sauraron kalaman Jajeri ba, rahoton Premium Times.

Gusau yace Mohammed Jajeri ba komai bane a harkar siyasar jihar Borno kuma ko a jam'iyyarsa babu wanda ya san da zamansa.

Kara karanta wannan

Kayar da Zulum abune mai saukin gaske: Dan takaran gwamnan PDP a Borno

Yace:

"Kada wanda ya kula karerayin da wani bakon dan takaran PDP ke yi a jihar Borno. Gwamna Babagana Umara Zulum na godewa dukkan masu amfani da kafafen sada zumunta wajen yada alkhairan da gwamnatin jihar keyi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan kwanakin nan dan takaran na PDP na hira da jarida yana sakin kalaman batanci kan Gwamna Zulum yayinda ake shirin zabe."
Kai karamin kwaro ne: Zulum ya mayarwa Jajari martani mai zafi
Kai karamin kwaro ne: Zulum ya mayarwa Jajari martani mai zafi Hoto: Governor of Borno/Premium Times
Asali: Facebook

Isa Gusau ya kara da cewa a shekaru 18 da suke siyasar Borno basu taba jin sunan wani Jajeri ba, bal ko yan jam'iyyar PDP basu san da shi ba.

"Ko a cikin masu ruwa da tsakin PDP a jihar, babu wanda ya san da zamansa," a cewarsa.

Kayar da Zulum abune mai saukin gaske: Dan takaran gwamnan PDP a Borno

Dan takaran Gwamnan jihar Borno karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Mohammed Jajari, yace ya lashe zaben fidda gwani ne saboda al'ummar Borno sun san zai iya tunbuke gwamnatin All Progressives Congress (APC) a 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan Borno a 2023: Dan takarar PDP ya zargi Zulum da son kai, ya sha alwashin tsige sa daga mulki

Yace mutane na ganin cewa Zulum yana wani aikin kwarai amma a kasa babu abinda yake yi illa korar ma'aikata.

Jajari yace zai lallasa Zulum wanda mutane ke ganin yayi kokari. Yace Zulum bai yi kokarin da ya cancanci a zabeshi ba a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel