Kayar da Zulum abune mai saukin gaske: Dan takaran gwamnan PDP a Borno

Kayar da Zulum abune mai saukin gaske: Dan takaran gwamnan PDP a Borno

  • Dan takarar Gwamnan Borno ya bayyana cewa tunbuke Zulum shine abu mafi sauki da zai yi
  • Mohammed Jajari yace babu wani aikin kirki da Gwamna Babagana Zulum yayi, kawai duk karya ce
  • Ya zargi gwamnatin Zulum da baiwa yan'uwa da abokan arziki kwangila maimakon yan kwangilan gaske

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dan takaran Gwamnan jihar Borno karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Mohammed Jajari, yace ya lashe zaben fidda gwani ne saboda al'ummar Borno sun san zai iya tunbuke gwamnatin All Progressives Congress (APC) a 2023.

Yace mutane na ganin cewa Zulum yana wani aikin kwarai amma a kasa babu abinda yake yi illa korar ma'aikata, rahoton Premium Times.

Yace:

"Lokacin da na yanki Fom karkashin PDP, wasu abokai na a Legas, Abuja, dss sun kirani cewa shin da Gwamna Zulum nike niyyar takara? Amma nace musu zan yanki tikiti kuma in kayar da shi."

Kara karanta wannan

Babban Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwani na 2023

Jajari yace zai lallasa Zulum wanda mutane ke ganin yayi kokari. Yace Zulum bai yi kokarin da ya cancanci a zabeshi ba a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

JAjari
Kayar da Zulum abune mai saukin gaske: Dan takaran gwamnan PDP a Borno Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewarsa:

"Wasu yan kallo daga waje na ganin ba zai yiwu ba, amma mu mafi akasarin mutan Borno mun san abune mafi sauki mu kayar da shi saboda babu wani abun kirkin da yake yi."
"Abu na farko zan kawar da matsalar tsaro; na biyu zan dawo da dukkan ma'aikatan da aka kora; na uku kuma zan tabbatar da cewa yan kwangilan gaske ake baiwa kwangila ba yan'uwa da abokai ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel