Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC ta soke amfani da wani muhimmin Fom a zaɓen 2023

Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC ta soke amfani da wani muhimmin Fom a zaɓen 2023

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ta soke amfani da Fom ɗin 'rahoton abun da ya faru' a dukkan zaɓukan Najeriya
  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shi ne ya bayyana haka a Ado Ekiti, ya ce ba za'ai amfani da Fom din a zaɓen Ekiti ba
  • Yakubu ya kara da neman goyon bayan Sarakunan gargajiya domin tabbatar da an gudanar da zaɓen lafiya

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ta soke amfani da 'Fom ɗin abun da ya faru' yayin gudanar da zaɓe a faɗin Najeriya.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Mahmud Yakubu, shi ne ya bayyana haka ranar Talata 31 ga watan Maris, 2022.

Farfesa Mahmud Yakubu.
Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC ta soke amfani da wani muhimmin Fom a zaɓen 2023 Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Farfesa Yakubu ya kuma bayyana cewa INEC ba zata yi amfani da Fom ɗin ba a zaɓen gwamnan jihar Ekiti, wanda zai gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya ce zai zaɓi wanda zai gaje shi a 2023, ya nemi goyon bayan gwamnoni

Mahmud Yakubu ya yi wannan jawabi ne a wurin taro da sarakunan gargajiya a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, karkashin majalisar sarakuna ta jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce INEC zata gudanar da zaben da aka ɗage na maye gurbin ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ekiti ta gabas rana ɗaya da zaɓen gwamnan jihar.

Idan baku manta ba, tun farko an shirya gudanar da zaɓen ɗan majalisar dokokin jihar a watan Maris 2021, amma bisa tilas aka ɗage shi saboda rikicin da ya hana kammala wa.

Muna bukatar goyon bayan sarakuna - Yakubu

Yayin taron, shugaban INEC da sauran yan tawagarsa sun nemi goyon baya da haɗin kan sarakunan gargajiya domin gudanar da zaɓe cikin zaman lafiya.

Basaraken Ilawe Ekiti, Oba Ajibade Alabi, da kuma Sarkin Emure Ekiti, Oba Adebowale Adebayo, sun sha alwashin ba da haɗin kai har a kammala zaɓe lami lafiya.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta Fito: Abin da Tambuwal ya faɗa wa shugaban PDP da wasu yan takara biyu kafin janye wa Atiku

A wani labarin kuma EFCC ta ayyana neman wani tsohon ɗan majalisa ruwa a jallo kan tsallake beli

Hukumar EFCC ta ayyana neman tsohon ɗan majalisar tarayya ruwa a jallo bisa wasu dalilai guda biyu.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, EFCC ta ce Mista Nzeribe, ya tsallake sharuddan beli da kotu ta ba shi kuma ya daina halartar shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel