Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

  • A yau ne wani bidiyo ya karade kafafen sada zumunta inda wasu matasa suka kashe tare da kone wata daliba a Sokoto
  • Lamarin ya faru ne sakamakon zargin dalibar da rubutun batanci ga manzon Allah SAW a shafin yanar gizo
  • A halin da ake ciki, rundunar 'yan sanda ta kamo wasu mutane biyu da ake zargin suna daga cikin wadanda suka yi aika-aikan

Jihar Sokoto - Akalla mutane biyu ne aka kama bisa laifin kashe wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta bayyana a ranar Alhamis, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar rundunar ‘yan sandan, an zargi Deborah Samuel, ‘yar matakin mataki na biyu a kwalejin, da yin wani rubutu a dandalin sada zumunta wanda ya nuna batanci ga manzon Allah (SAW).

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Yadda aka kama wadanda suka kashe daliba a Sokoto
Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibai da ake zargin ta zagi Annabi | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Rundunar ‘yan sandan ta ce daliban un dauki matashiyar da karfin tsiya daga wurin jami’an tsaro da hukumomin makarantar, suka kashe ta tare da konata Kurmus.

Wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu maza suke jifanta da sanduna tana kwance a kasa sanye da kaya mai launin ja, inji rahoton Tribune Online.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu faifan bidiyo sun kuma nuna wata wuta da ta tashi yayin da wani mutum ya fuskanci kyamara, yana mai cewa ya kashe ta kuma ya kone ta, yana kuma rike da kwalin ashana.

Rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin cewa za ta gano wadanda aka gani a faifan bidiyon da aka yada a shafin Twitter, kuma za a kamo su nan ba da dadewa ba, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda a Sokoto, Sanusi Abubakar ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

A cewar Malam Abubakar, an rufe makarantar tare da tura karin jami’an ‘yan sanda yankin.

Daliban kwalejin ilimin Shehu Shagari sun kashe daliba kan zargin batanci ga Annabi

A tun farko kunji cewa, an kashe wata dalibar kwaljin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi).

21st CENTURY CHRONICLE ta ruwaito cewa an kashe dalibar mai suna Deborah bayan an bukaci ta janye kalamanta amma taki. Rahoton ya kara da cewa wannan abu ya faru ne ranar Alhamis da safe.

Yanzu dai gwamnatin jihar Sokoto ta rufe makarantar, riwayar TVCNews. Bidiyoyi a kafafen sada zumunta sun nuna yadda dalibai suka yiwa dalibar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel