Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

  • Mrs Ngozi Umeoji, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APGA, Chuma Umeoji ta rasu
  • Mahaifiyar Dan Majalisar ta rasu ne misalin kwana daya bayan ta yi wa matan da mazajensu suka rasu rabon shinkafa, kudi da wasu kayan abinci
  • Iyalanta sun tabbatar da rasuwarta cikin wata sanarwa da suka fitar ta bakin hadimin Chuma Umeoji inda suka ce mutumiyar kirki ce mai taimakon marasa galihu

Jihar Anambra - Mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.

Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.

Kara karanta wannan

Karar kwana: An shiga jimami yayin da matar tsohon mataimakin gwamna ta rasu

Mahaifiyar dan majalsa ta rasu awa 24 bayan ta bawa matan da mazajensu suka rasu sadaka
Mahaifiyar dan majalisa ta rasu kwana guda bayan yi wa mutanen garinsu rabon kudi da kayan abinci. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ofishin watsa labarai na dan majalisar ta fitar a ranar Talata ta ce:

"Muna sanar da rasuwar Cif Lady Ngozi Umeoji, na gidan Umeoji wacce a rasu a ranar Lahadi, 6 ga watan Fabrairun 2022, kusan bayan awa 24 bayan farantawa matan da mazajensu suka rasu rai a Ezinfite.
"Rasuwarta ya girgiza kowa musamman mutanen da ke amfana da aikin alherinta da a farantawa rai a baya-bayan nan yayin da ta yi sadaka a garinsu na Ezinifite, Aguata a ranar 5 ga watan Fabrairun 2022, har yanzu suna ta godiya.
"Ta yi rayuma mai tattare da darasi da za a koya. Tana daya daga cikin mutanen kirki da suka rayu cikinmu, tamkar Mother Theresa ta zamaninmu
"Mata ce wacce ta sadaukar da rayuwanta domin kyautata wa wasu. Garin Ezinifite, Jihar Anambra ya yi babban rashi kuma soja Yesu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta tabbatar da Farfesa Ayo Omotayo matsayin sabon shugaban NIPSS

Sanarwar da aka fitar bai bayyana shekarun marigayiya Mrs Umeoji ba.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel