Jigawa: An Tsinci Gawar Wani Ɗan Shekara 55 Da Ya Mutu a Hanyarsa Na Zuwa Kasuwa

Jigawa: An Tsinci Gawar Wani Ɗan Shekara 55 Da Ya Mutu a Hanyarsa Na Zuwa Kasuwa

  • Hukumar tsaro na NSCDC reshen Jihar Jigawa ta gano gawar wani mutum dan shekara 55, Isyaku Shuaibu a gefen titi
  • Kakakin NSCDC na Jihar Jigawa, Adamu Shehu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba
  • Shehu ya ce sun samu kirar neman dauki ne a ranar Talata kuma da jami'ansu suka isa wurin sun tsinci gawar Shuaibu a gefen titi

Kiyawa, Jigawa - Jami'an hukumar tsaro na NSCDC sun gano gawar wani mutum dan shekara 55, Isyaku Shuaibu, a karamar hukumar Kiyawa na Jihar Jigawa.

The Punch ta rahoto cewa kakakin hukumar NSCDC, Adamu Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce abin ya faru ne a ranar Talata misalin karfe 9.30 na safe.

Kara karanta wannan

Innalilahi: Mutum 7 Sun Mutu Sakamakon Gobara Da Ta Auku a Gidan Man Fetur a Jigawa

Jigawa: An Tsinci Gawar Wani Ɗan Shekara 55 Da Ya Mutu a Hanyarsa Na Zuwa Kasuwa
An Tsinci Gawar Wani Ɗan Shekara 55 Da Ya Mutu a Hanyarsa Na Zuwa Kasuwa a Jigawa. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Shehu ya ce sun samu kiran neman dauki, hakan yasa suka tura tawagarsu ta lafiya zuwa wurin da abin ya faru.

"Da isarsu, sun gano gawar Shuaibu a gefen titi a hanyar Kiyawa - Andaza, kimanin kilomita biyu daga garin Andaza.
"Binciken farko da aka yi a wurin da abin ya faru ya nuna cewa babu alamar rauni na zahiri. Don haka, an kai gawar zuwa babban asibitin Dutse, don bincike," a cewar sanarwar.

Ya bar gida ne domin ya tafi cin kasuwar Sara, in ji 'yan uwan Shuaibu

An jiyo wani daga cikin yan uwan mamacin na cewa Shuaibu ya bar gida ne da niyyar zuwa kasuwar Sara, wani kasuwa da ake ci kowanne ranar Talata, rahoton The Punch.

Iyalansa sun ce abin ya daure musu kai lokacin da aka ce an gano gawarsa a gefen titi.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Shehu ya ce kwandan rundunar NSCDC na jihar, Mustapha Talba, ya tura jami'ai domin su yi bincike a garin.

Ya bukaci mazauna garin su kwantar da hankulansu, a yayin da ake kokarin gano abin da ya yi sanadin rasuwar mutumin mai shekaru 55.

Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

A wani labarin, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

Asali: Legit.ng

Online view pixel