Mahaifina Ya Min Gargaɗi Game Da Zuwa Ƙauyenmu, Ya Ce Mayu Za Su Cinye Ni, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

Mahaifina Ya Min Gargaɗi Game Da Zuwa Ƙauyenmu, Ya Ce Mayu Za Su Cinye Ni, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

  • Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Dele Momodu ya bayyana dalilinsa na kin zuwa kauyensu akai-akai, Ihievbe da ke karamar hukumar Owan ta gabas a Jihar Edo
  • Kamar yadda ya ce, mahaifinsa ne ya ja masa kunne akan kada ya je mayu maza da mata da ke kauyensu su lamushe shi, hakan yasa tun suna yara ba ya kai su kauyen
  • A cewarsa, a shekarar 2014 da za su je kauyen, sai da mahaifiyarsa ta dinga kuka, tana tsoron kada su halaka shi amma hakanan ya je saboda ya san tushensa

Legas - Dele Momodu, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya sanar da dalilinsa na kin ka ziyara kauyensu, Ihievbe da ke Owan ta gabas a Jihar Edo akai-akai, The Punch ta ruwaito.

Dan takarar ya ce mahaifinsa ya ja kunnensa inda ya ce mayu maza da mata da ke kauyen za su cinye shi.

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Mahaifina ya min gargadi game da zuwa kauyenmu, ya ce mayu za su cinye ni, Dan Takarar Shugaban Kasa
Mahaifina ya ja kunne na akan zuwa kauyenmu da ke Edo, ya ce mayu zasu iya cinye ni, Dele Momodu. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Momodu ya yi wannan bayanin ne yayin da ya bayyana a shirin Morning Talk na Arise TV a ranar Talata inda ya ke amsa tambaya akan dalilinsa na bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a Ihievbe da ke Jihar Edo.

Ya ce babu inda Tinubu da Osinbajo za su shiga da ba zai iya kwana ba

Momodu ya kada baki ya ce:

“Mahaifina ya yi rayuwarsa har ya mutu a Ile-Ife. Lokacin da muka tambaye shi dalilinsa na kin kai mu Ihievbe, Edo, cewa ya yi saboda mayu maza da mata da ke kauyen zasu iya cinye mu.
“A lokacin da na sanar da mahaifiyata cewa zan je kauyen a 2014, fashewa ta yi da kuka. Ta ce za su halaka ni. Ni kuma na ce mata mutane na ne, idan sun halaka ni babu komai, sai na tafi.

Kara karanta wannan

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

“Daga nan ne na gane tushe na. Kuma sun tarbemu kwarai, wanda na ji dadin tarbar. Babu inda Tinubu ko Osinbanjo zai shiga da ba zan iya kwana ba. Ina da karfi sosai a kudu maso gabas.”

Ya samu tarba ta musamman daga mutanen kauyen

A ranar Asabar, 17 ga watan Afirilu Momodu ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a kauyensu, Ihievbe da ke karkashin karamar hukumar Owan ta gabas a Jihar Edo inda ya ce yana cikin wadanda suka cancanci maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Momodu ya samu tarba daga ayarin mutane dayawa, inda ya ce shi ba gwamna ba, sanata ko minista, amma ya samu damar zama da mutane masu daraja, hakan ya sa ya ce ya cancanci zama shugaban kasa.

Shugaban kauyen Ugba da ke Ihievbe, Pa. Rufus Aigbevbole ya kwatanta Dele Momodu a matsayin dansu wanda suke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel