Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

  • Jigon jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya kai ziyara ga babban malamin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi
  • Tinubu ya isa ga malamin ne a yayin da ya kai ziyarar jaje jihar Kaduna bayan harin jirgin kasa da ya faru a makon da ya gabata
  • Shehin malamin ya sakawa dan siyasar wanda ke neman shugabancin kasar albarka tare da yi masa tofin addu'o'i

Kaduna - Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Dahiru Bauchi.

Tinubu wanda ke neman takarar shugabancin kasar a zaben 2023 karkashin inuwar APC, ya ziyarci Shehin Malamin ne a yayin ziyarar jaje da ya kai jihar Kaduna a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu.

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi
Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A daya daga cikin hotunan ziyarar tasa wanda tuni suka karade shafukan sadarwa, an gano Tinubu durkushe a gaban jigon na darikar Tijjaniyya yayin da shi kuma ya dafa kansa sannan ya saka masa albarka tare da yi masa tofin addu’o’i.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter wanda ke tabbatar da ziyarar da ya kaiwa Shehin Malamin, Tinubu yace sun tattauna lamura da dama.

Sai dai ya ce sun fi karkata ga yadda za a yi amfani da koyarwar addinin Islama wajen kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi musamman a wannan wata ta Ramadana.

Tinubu ya ce:

“Kafin na bar Kaduna, na kuma ziyarci mai girma Sheikh Dahiru Bauchi. Tattaunawarmu ta tabo batutuwa da dama amma ta karkata ga yadda za a iya amfani da koyarwar Musulunci wajen kawo karshen tashe-tashen hankula da rigingimu a kasar nan musamman a wannan wata mai alfarma.”

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

A gefe guda, mun kawo cewa Bola Tinubu, ya koka kan yawan hare-haren ta’addanci da kasar ke fuskanta, inda ya ce Najeriya na zubar jini.

Tinubu wanda ya ziyarci jihar Kaduna domin yiwa gwamna Nasir El-Rufai jaje a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu, ya ce akwai bukatar hada hannu domin yakar fashi da makamai da kuma ta’addanci.

Ya yi Allah-wadai da harin da yan bindiga suka kai kan jirgin kasar Kaduna a makon da ya gabata, inda ya bayyana lamarin a matsayin abun kunya, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel