Maganin kiriniya: Bidiyon kakan da ya danna jikansa a bokiti ya jawo cece-kuce a intanet

Maganin kiriniya: Bidiyon kakan da ya danna jikansa a bokiti ya jawo cece-kuce a intanet

  • Wani faifan bidiyo mai ban dariya ya nuna wani tsoho yayin da yake dauke da yaro a cikin wani shudin bokiti, yana yawo da shi kamar jakar hannu
  • A cikin faifan bidiyo mai ban dariya, an ga mutumin a cikin wani babban kantin siyayya inda watakila ya je siyayyar kayayyaki
  • Bidiyon ya samu tsokaci mai ban dariya a kafar Instagram inda aka yada shi, kana wasu sun yabi aikin wannan tsoho

An ga wani mutum yana yawo a wani babban kantin siyayya dauke da yaro karami a cikin wani shudin bokiti, abin da ya sa wasu dariya a shafin intanet.

Mutumin da aka ce kakan yaron ne ya zagaya cikin kantin tare da yaron yana leko da kansa daga cikin bokitin.

Kara karanta wannan

Kwalliya iya kwalliya: Ma'abota kafafen sadarwa sun tofa albarkatun bakinsu kan kwalliyar Amarya

Kaka da yaro
Maganin kiriniya: Bidiyon yadda wani kaka ya danna jikansa a bokiti ya jawo cece-kuce | Hoto:@baabyjaamie and @pubity
Asali: Instagram

Yaron sai murmushi yake

Sai dai ga dukkan alamu yaron dai na jin dadin zaman bokitin, yayin da aka gan shi yana murmushi irin na farin ciki yayin da tsohon ke dauke dashi kamar jakar hannu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon ya yi tafiya a cikin tsakani sosai kamar abin da yake yi ba wani abu ne da ba a saba gani ba.

Bidiyon ya haifar da cece-kuce mai ban dariya a tsakanin masu amfani da shafin Instagram.

Kalli bidiyon:

Masu amfani da Instagram sun yi martani

Bugu da kari, masu amfani da shafin sada zumunta na Instagram sun mayar da martani ga bidiyon bayan da @pubity ya yada shi.

Karanta kadan daga cikin martanin jama'a:

@amiee_p:

"Ina mamakin waye wannan ya tuna min lol."

@lgrace118 ya amsa:

"Ah yaro a bokiti a kantin kayayyaki."

Kara karanta wannan

Ba zan ci kudinku ko kwandala ba: Gwamnan PDP ya yiwa 'yan jiharsa alkawari

@fattygatty yayi sharhi:

"Wannan ya yi kyau, amma yi tunanin ganin wannan ba tare da karin bayani ba lol."

@young.child81 ya ce:

"Mutumin nan yana ma da karfi."

Kwalliya iya kwalliya: Ma'abota kafafen sadarwa sun tofa albarkatun bakinsu kan kwalliyar Amarya

A wani labarin mai ban dairiya, farashin kudin kwalliyar zamani da ake yiwa amare da kawayensu na farawa daga N5000 zuwa N100,000, dangane da mai kwalliyar da irin kayan da akayi amfani.

Amma wasu masu sana'ar kwalliyan kan shiga uku idan suka tafka kuskure musamman kan amare.

Da alamun irin haka ya faru a wani bidiyon da ya bazu a soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel