Kwalliya iya kwalliya: Ma'abota kafafen sadarwa sun tofa albarkatun bakinsu kan kwalliyar Amarya

Kwalliya iya kwalliya: Ma'abota kafafen sadarwa sun tofa albarkatun bakinsu kan kwalliyar Amarya

  • Bidiyon wata sabuwar Amarya a ranar aurenta ya yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya janyo cece-kuce
  • A bidiyon da aka daura a shafin Instagram, an ga amaryar da wata irin kwalliya mai yawan gaske
  • Mutane da dama a kafafen ra'ayi da zumunta sun yi kira ga a kama wanda ya yiwa Amarya wannan kwalliya

Farashin kudin kwalliyar zamani da ake yiwa amare da kawayensu na farawa daga N5000 zuwa N100,000, dangane da mai kwalliyar da irin kayan da akayi amfani.

Amma wasu masu sana'ar kwalliyan kan shiga uku idan suka tafka kuskure musamman kan amare.

Da alamun irin haka ya faru a wani bidiyon da ya bazu a soshiyal midiya.

Kwalliya iya kwalliya
Kwalliya iya kwalliya: Ma'abota kafafen sadarwa sun tofa albarkatun bakinsu kan kwalliyar Amarya Hoto: @krakstv
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

A bidiyon da @krakswtv ta saki, amaryar ta sha kwalliya mai ban yawa.

Sabanin foundation da yayi yawa, jan baki da aka daura mata ya yi yawa.

Kalli bidiyon:

Tsokacin mutane:

Hussain M Namadi Ringim yace:

"Yan ba'a gani a kale ne yan sa ido yan Nigeria"

Nana Maryama Aliyu yace:

"Wannan Anya ba tayi aikin wanke wanke da shara a kasar Indai ba."

Zakari D Bocho yace:

"Anya wan Nan mutun ne kuwa? Agaskiya wan Nan amaryan za asha kallon kallo da Yan uwan ango agurin budankai, inba amayarda hankaliba ranan biki iska zasu tashi Akan mata."

Abubakar Isah Bichi yace

"Wannan ai dole Ace wani abu se kace 'yar bararoji"

Umar Sani Anwar:

"Ni ma kasa gane matata nayi. Haka ta zo ta wuce, ina nemanta."

Asali: Legit.ng

Online view pixel