Mubarak Bala yayi watsi da lauyansa a kotu, ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su

Mubarak Bala yayi watsi da lauyansa a kotu, ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su

  • Bayan wata da watanni, an cigaba da sauraron karar Mubarak Bala a wata babbar kotu dake jihar Kano
  • Mubarak Bala ya amsa jerin laifukan da ake zarginsa da su na batanci ga addinin Musulunci
  • An tsare Mubarak Bala ne bisa kalaman da ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda ya janyo cece-kuce

Kano - Kotu a jihar Kano ranar Talata ta bada umurnin cigaba da tsare Mubakar Bala a gidan gyaran hali sakamakon gazawar lauyoyinsa na gabatar da hujjojin tabbatar da cewa yana fama da rashin lafiya.

Hakazalika kotun tace ana cigaba da tsareshi ne don tsare rayuwarsa.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa Mubarak Bala ya amsa laifuka 14 da ake tuhumarsa da su.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari

Rahoton ya kara da cewa yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook inda yayi kalaman batanci ga addinin Musulunci.

Mubarak Bala
Mubarak Bala yayi watsi da lauyansa a kotu, ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su Hoto: BBC Hausa
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sabanin da ya auku tsakanin Mubarak Bala da Lauyansa

Bayan amsa duka laifukan batancin da ake tuhumarsa da shi, lauyan Mubarak, James Ibor, cikin mamaki ya bukaci kotu ta bashi daman sa labule da shi don masa bayanin abinda ka iya biyo bayan amsa laifin da yayi.

Bayan nuna alamun ya gamsu, Lauyan ya sanarwa Alkali cewa Mubarak Bala ya canza ra'ayinsa, yana son sauya amsar da ya bada.

Sai Alkali mai shari'a ya tambayi Mubarak shin ko haka lamarin yake, Mubarak Bala yace sam, ba zai sauya amsar da ya bada na amincewa da laifukan da ake tuhumarsa da su ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon wani mutum da ya rasa hannu, ido, kunne kuma 'dansa ya rasa hannu da kafa a hadarin mota

Bayan jaddada masa nauyi da tasirin amsa laifinsa da Alkali yayi, Mubarak yace tabbas ya fahimci komai kuma ba tursasashi akayi ba, kuma ra'ayinsa ne.

Me Mubarak Bala yayi?

A ranar 28 ga Afrilu, 2020, Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta kama Mubarak Bala bisa zarginsa da yin batanci ga addinin Islama.

An kama matashin ne bayan wata kungiyar lauyoyi ta shigar da korafi a ofishin kwamishinan 'yan sanda na Kano bisa zarginsa da cewa ya zagi annabi Muhammad a shafinsa na 'facebook'.

Korafin lauyoyin, mai dauke da sa hannun S.S Umar ya bayyana cewa, "mun kawo korafi ne a kan wani mai suna Mubarak Bala dan unguwar Karkasara a Kano.

"An haifi Mubarak a gidan Musulunci amma saboda wasu dalilai na kashin kansa sai ya zabi ya bar addinin, ya zama marar addini, a 2014. Tun da ya bar addini ya ke wallafa sakonnin da basa yi wa Musulmai dadi a shafinsa na 'facebook'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel