Kaduna: 'Yan sanda sun kama wani matashi da ya yi batanci ga Annabi a dandalin sada zumunta
Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta kama wani matashi mai suna Mubarak Bala bisa zarginsa da yin batanci ga addinin Islama.
An kama matashin ne bayan wata kungiyar lauyoyi ta shigar da korafi a ofishin kwamishinan 'yan sanda na Kano bisa zarginsa da cewa ya zagi annabi Muhammad a shafinsa na 'facebook'.
Korafin lauyoyin, mai dauke da sa hannun S.S Umar ya bayyana cewa, "mun kawo korafi ne a kan wani mai suna Mubarak Bala dan unguwar Karkasara a Kano.
"An haifi Mubarak a gidan Musulunci amma saboda wasu dalilai na kashin kansa sai ya zabi ya bar addinin, ya zama marar addini, a 2014. Tun da ya bar addini ya ke wallafa sakonnin da basa yi wa Musulmai dadi a shafinsa na 'facebook'.
Wata majiya ta ce wasu jami'an 'yan sanda ne guda biyu, a cikin fararen kaya, suka je har gida suka kama Mubarak tare da tafiya da shi ofishinsu mafi kusa da gidan da yake zaune a Kaduna.
Wani mamba a wata kungiya da Mubarak ke zaman shugaba ya shaidawa manema labarai cewa suna bukatar a gaggauta sakinsa ba tare da wani bata lokaci ba.
"Mun damu matuka da kama shugabanmu, Mubarak Bala, da aka yi.
DUBA WANNAN: Mun sakarwa shugabannin Boko Haram bama-bamai yayin da suke taro a jihar Borno - DHQ
"Watakila rundunar 'yan sandan Kaduna za ta mika shi hannun 'yan sanda a Kano, inda ake so a gurfanar da shi a gaban kotu saboda suna aiki da dokar Musulunci ta kashe ma su batanci ga addini.
"Mu na rokon babban sifeton rundunar 'yan sanda da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, a kan su saka baki domin a gaggauta sakinsa," a cewarsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng