Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70

Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70

  • An shirya gagarumar liyafa domin bikin murnar cikar Kwamared Adams Oshimohole shekaru 70 da haihuwa
  • Wurin liyafar ya cika da hotuna masu kayatarwa tare da kada-kade masu nishadantarwa inda iyalin dan siyasan suka bayyana
  • Sai dai duk da shekarun Oshiomhole, an ga yadda ya zage tare da dagewa wurin nuna kwarewarsa wurin rawa a liyafar

An shirya wa Adams Oshiomhole bikin murnar cika shekaru 70 da haihuwa kuma dan siyasar ya nishadantar da bakinsa da irin salon rawansa mai matukar kayatarwa.

Fitaccen dan siyasan kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya cika shekaru 70 a duniya a ranar 4 ga watan Afirilu.

Wani faifan bidiyo da ya bayyana daga wurin taron ya nuna tsohon gwamnan jihar Edo yana rawa tare da zukekiyar matarsa, ​​Lara Oshimhole.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci zaman Tafsirin AlQur'ani yau

Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70
Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

Ya kuma nuna yadda gwiwowinsa ke da karfi duk da kuwa shekarunsa ganin yadda ya yi kasa kasa yayin da yake rawa.

Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70
Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70
Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70
Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

'Yan Najeriya sun yi martani

Tuni bidiyon rawan Adams Oshiomhole ya watsu a soshiyal midiya kuma 'yan Najeriya suka dinga bayyana ra'ayoyinsu game da hakan.

Yayin da wasu ke kwarzanta Oshiomhole, wasu sun kwatanta shi da dan takarar shugabancin kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya cika shekaru 70 a kwanaki kadan da suka gabata.

Ga wasu daga cikin martanin 'yan Najeriya:

Ninuoola ta ce: "Don Allah a taimaka a kira min Kawu Tinubu, na ji an ce shi ma ya cika shekaru 70 a kwanakin da suka gabata."
Adornareaccessoriesng cewa yayi: “Matarsa ta rasa yadda za ta iya cimmasa a irin tsarin rawan nan."

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Geesgotjokes cewa ta yi: “Oshiomole ya dade yana gwagwarmaya tun daga lokacin fafutukar kare hakkin dan Adam."
Chistar_maris ta ce: “Shin Tinubun ku zai iya rawa kamar haka?"

Hotunan Seyi Tinubu yana zantawa da Dangote, Osinbajo da Obasanjo a bazden mahaifiyar Otedola

A wani labari na daban, Asiwaju Bola Tinubu, Jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa kuma dan takarar shugabancin kasa a shekarar 2023, bai samu hallartar shagalin bikin zagaoyowar ranar haihuwar mahaifiyar fitaccen biloniya Femi Otedola ba da aka yi a Epe dake jihar Legas.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo; tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki; Attajirin Afrika, Aliko Dangote, suna cikin manyan baki da suka halarci taron.

Duk da haka, Seyi, ɗan Tinubu, wanda ya fi yin fice, ya kasance a wurin taron, yana warwasawa tare da zantawa da manyan mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel