Abubuwa 7 da ya kamata a sani a tarihin Sanata Dansadau wanda ya tsige Imam Nuru Khalid

Abubuwa 7 da ya kamata a sani a tarihin Sanata Dansadau wanda ya tsige Imam Nuru Khalid

  • Saidu Muhammad Dansadau ne shugaban kwamitin masallacin ‘yan majalisa da ke Apo a Abuja
  • Sanata Dansadau fitaccen ‘dan siyasa ne, manomi kuma ‘dan kasuwa wanda ya fito daga Zamfara
  • Tsakanin 1999 da 2007, Dansadau ya na cikin Sanatocin da suka yi suna wajen adawa da gwamnati

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta kawo takaitaccen tarihin wannan mutumi wanda ake ta maganarsa bayan tunbuke Nuru Khalid daga limanci.

1. Haihuwa da karatu

A shekarar 1953 aka haifi Sa’idu Muhammad Dansadau. Nan da watanni biyu zai cika shekara 69 a Duniya.

Bayan karatun firamare da sakandare, Dansadau ya yi digiri a bangaren koyarwa. Daga baya kuma ya samu shaidar PGD a harkar gudanar da aiki.

Sa’idu Muhammad Dansadau ya fara aiki ne a matsayin malamin makaranta. Daga baya ya rungumi harkar noma kafin ya shiga cikin siyasa.

Kara karanta wannan

Dattijon arewa ya yi fallasa, ya sanar da abinda Gumi ya fadi wa 'yan bindigan daji

2. Siyasa

A shekarar 1981, Sa’idu Dansadau ya rike sakataren NPN na jihar Sokoto. A lokacin jam’iyyar ta kafa gwamnati a jihar Sokoto da tarayyar kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dansadau ya rabu da wannan mukami a 1983, a lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin Shehu Shagari, daga baya ya dawo siyasa a 1992.

Da aka fito da NRC da SDP, Dansadau ya nemi kujerar majalisar tarayya a zaben 1992 amma ya sha kashi. A lokacin yana tare da Umaru Shinkafi.

3. Majalisar dattawa

Bayan an koma farar hula a 1999, Dansadau ya lashe zaben Sanatan Zamfara ta tsakiya, ya tafi majalisar dattawa, ya zarce a wannan kujera har 2007.

Kafin ya bar majalisa ya rike sakataren Sanatocin Arewa, ya shiga kwamitocin kula da dukiyar kasa, kiwon lafiya, kwadago, kasuwanci, da harkar gida.

Sanata Dansadau a taron NRM
Saidu Muhammad Dansadau Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Sanatan yana cikin wadanda suka taso Adolphus Wabara har yayi murabus. Kuma da su aka dage wajen rusa maganar tazarcen shugaba Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

4. Barin siyasa da dawowarsa

Bayan Dansadau ya bar majalisar dattawa a 2007, sai aka ji ya bada sanarwar ya fice daga ANPP, kuma ya daina siyasa bayan shekaru kusan 27 ana gwabzawa.

A 2010 aka nada shi cikin kwamitin da ya yi bincike kan badakalar harkar filaye a birnin tarayya. Bayan shekaru da yin wannan, sai Dansadau ya dawo siyasa.

5. Kafa sabuwar jam’iyya

Saidu Muhammad Dansadau ya kafa jam’iyyar NRM da nufin doke PDP da APC a 2019. Tsohon Sanatan ya yi takarar gwamnan Zamfara a zaben amma bai ci ba.

An taba rahoto shi ya na cewa an yi tunanin Muhammadu Buhari zai kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye Najeriya, amma gwamnatinsa ta APC ta gaza.

6. Rikicin Zamfara

Dattijon ya na cikin wadanda suka yi magana a kan rashin tsaron da ake fama da shi a Zamfara, ya na ganin rashin adalci ya jawo rikicin, kuma dole kowa ya tuba.

Kara karanta wannan

Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja

Saidu Dansadau ya taba zargin tsohon Sarkin Dansadau, Hussaini Umar da hannu a kashe-kashen da ake yi. Zargin da Wazirinsa, Mustapha Umar bai kyale ba.

7. Dansadau ya kori Imam Khalid

Ku na da labari cewa Sheikh Nuru Khalid ya rasa kujerarsa ne saboda wata huduba da ya gabatar a kan halin rashin tsaro ganin yadda aka tare jirgin kasa kwanaki.

Kwamitin da ke kula da masallacin a Apo a karkashin jagorancin Sa’idu Dansadau ta dakatar da shi. Daga bisani sai aka ji cewa an kore shi daga limanci gaba daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel