Abinda Gumi ya sanarwa ‘yan bindiga da muka hadu da su a dajikan jihohin Arewa 8, Mamban NEF

Abinda Gumi ya sanarwa ‘yan bindiga da muka hadu da su a dajikan jihohin Arewa 8, Mamban NEF

  • Mamba a kungiyar dattawan arewa, Usman Yusuf, ya sanar da yadda arangamarsu da 'yan bindiga ta kasance a dajikan jihohi 8 na Arewa
  • Tsohon sakataren hukumar Inshorar lafiya ta kasan, ya ce Gumi ya sanar da su kisa, sata, lalata dukiyar mutane da ta gwamnati ba mafita bace
  • Kamar yadda Yusuf ya tabbatar, ya ce dukkan matsalar tsaron Najeriya ta cikin gida ce, kuma a cikin gida ya dace a magance ta

Wani mamba a kungiyar dattawan Arewa, Usman Yusuf, ya bayyana abinda fitaccen malamin addinin Islama Ahmad Gumi, ya fada wa ‘yan bindiga da suka hadu da su a cikin dajikan jihohin Arewa takwas.

A cewar dattijon, Gumi ya shaida wa ‘yan fashin wadanda yanzu aka ayyana a matsayin 'yan ta'adda, cewa kisa, fyade, raunata jama'a da kona dukiyoyin jama’a da na gwamnati ba abu ne da za a amince da su ba, kuma babu hujja kan abinda suke yi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023

Abinda Gumi ya sanarwa ‘yan bindiga da muka hadu da su a dajikan jihohin Arewa 8, Mamban NEF
Abinda Gumi ya sanarwa ‘yan bindiga da muka hadu da su a dajikan jihohin Arewa 8, Mamban NEF. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Ya ce shi da Gumi sun tsunduma cikin daji inda suka ziyarci ‘yan bindigar a cikin dajikan jihohin Arewa maso Yamma da kuma jihohin Arewa ta tsakiya uku domin su “saurari” kokensu.

Dan kungiyar NEF din yayi magana ne a daren ranar Litinin lokacin da ya bayyana a matsayin bako a shirin ‘siyasarmu a yau’ na gidan talabijin na Channels Television.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekarar 2019 ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kori Yusuf a matsayin babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta kasa.

Yadda muka shiga surkukin daji, maboyar miyagu

Da yake magana a daren ranar Litinin, Yusuf ya ce,

“Yan Najeriya na bukatar su lura; muna cikin wani mawuyacin hali. Al’amarin tsaro a kasar nan ya wuce gona da iri. Ni likita ne, Sheikh Gumi likita ne, maimakon mu zauna a ofisoshinmu mu ji labarai, sai muka je ramin zakuna; mun ziyarci jihohi takwas, a cikin dazuka biyar a kan gaba a jihohin Arewa maso Yamma da uku a jihohin Arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

“Me yasa muka tafi? Dalilin da ya sa muka je shi ne mu saurare su… mun je saurare. Abin da muka ji a ko'ina, matsalolin cikin gida ne kuma dole ne a samo mafita a cikin gida. A cikin jihohin takwas da muka je babu wani daga cikin ‘yan fashin da ya gaya mana cewa suna da matsala da sojojin Najeriya ko kuma gwamnatin tarayya.
“Mafi girman matsalolin koyaushe suna cikin gida. Muna bukatar mu fahimci hakan. Wannan shi ne babbar matsalar da muka gani a makon da ya gabata, ba mu iya bacci, muna cikin tashin hankali.'

Duk da shi ma ya na sukar Gwamnati, Ahmad Gumi ya soki hudubar Sheikh Nuru Khalid

A wani labari na daban, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya tofa albarkacin bakinsa game da abin da ya faru na sauke Shiekh Nuru Khalid daga limanci a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

Kamar yadda labari ya zo mana, babban malami, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana da jaridar Daily Post a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilu 2022.

A ra’ayin Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, Nuru Khalid ya yi kuskure a hudubar da ya yi, ya na mai cewa jama’a za su ki kada kuri’arsu a filin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel