Cikakkiyar hudubar Juma’ar da ta jawo aka dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Apo

Cikakkiyar hudubar Juma’ar da ta jawo aka dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Apo

  • An dakatar da babban limamin masallacin rukunin gidajen ‘yan majalisa na Apo da ke garin Abuja
  • Sheikh Nuru Khalid ya rasa kujerarsa ne saboda wata huduba da ya gabatar a kan halin rashin tsaro
  • Kwamitin da ke kula da masallacin a karkashin jagorancin Sanata Sa’idu Dansadau ta dakatar da shi

Legit.ng Hausa ta saurari wannan huduba ta Sheikh Nuru Khalid, ta fassara ta zuwa harshen Hausa. The Cable ta kawo asalin hudubar cikin harshen Ingilishi.

“Shin babu wanda zai dauki laifi ne? Ina ganin cewa dukkaninmu mun gaza. Ma’ana – Na gaza a matsayin Limami, na gagara fahimtar da ku cewa rai na da daraja.”
“Dukkanku kun gaza a matsayinku na iyaye wajen nunawa ‘ya ‘yanku cewa kashe-kashe ba abu mai kyau ba ne. Shugabanni, ‘yan siyasa, da gwamnoni sun gaza.”

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

Shugaba Buhari ya ba mu kunya

“Musamman kuma mai girma shugaban kasar tarayyar Najeriya, ya ba mu kunya.”
“Mu na da bidiyonka ka na fadawa ‘Yan Najeriya cewa sojojinmu ba su gaza ba, su na duk abin da ake bukata na shawo kan matsalar tsaro da zarar ka samu mulki.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An ba ka shekaru hudu, har da kari amma ana kashe mutane kamar tsuntsaye. Kisan rai ya na nema ya zama abin da aka saba da shi a karkashin mulkinka (Buhari).”

Ni zan fito, in fada maka - Nuru Khalid

“Babu wani ‘Dan Najeriya da zai fada maka? Ni zan dauki nauyin fada maka, kuma in saurari matakin da zai biyo baya domin rai da dukiyar jama’a na gaba da komai.”
Nuru Khalid
Sheikh Nuru Khalid Hoto: newsdigest.ng
Asali: UGC
“Bari in fada maka shugaban kasa, a mulkinka, ‘yan bindiga na tatsar haraji a hannun ‘Yan Najeriya, bayan doka ta ce ba a ba kowa kudi sai gwamnati.”

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Me ya hana Buhari zuwa Kaduna yin ta'aziyya?

“Ku je ku duba tarihi. Sau nawa ya je Kaduna domin kamfe? Ko bai je Kaduna ya yi kamfe ba? Bai je Kaduna a lokacin da yake neman kuri’a daga hannunsu ba.”
“(Buhari) bai je Kaduna ba. Amma bam ya tashi a titin jirgin kasan zuwa Kaduna, bai iya zuwa ya duba su ba. Amma zai zauna ya na yin tir, ya na Allah-wadai.”
“Kowa a Najeriya zai iya Allah wadai a kan munanan abubuwan da ke faruwa, ‘yan ta’addan ne kurum ba za su yi Allah-wadai ba.” So mu ke kayi mulki, ba tir ba.”

Me ya kamata shugaban kasa ya yi?

“Ka bada umarnin ayi ram da wadannan ‘yan ta’adda a duk inda suke, a dakile inda suke samun kayan aiki, a kama duk wasu masu taimaka masu, a hukunta su.”
“Amfanin Gwamnati shi ne iko. Jama’a, ba a yin gwamnati da ruwan sanyi. Gwamnati na amfani da karfinta ta kama, kashe, addaba…haka mu ke so ayi wa ‘yan ta’adda."

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

“Duk mai neman muzgunawa talakan Najeriya da ke zaune a cikin aminci, gwamnati ta nuna karfinta, ta wulakanta shi. Talaka ya saye zaman lafiya har da kudinsa.”

Martanin 'Yan Najeriya

Rahoto ya nuna 'yan Najeriya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu sun yi martani ga gwamnati kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid da aka yi daga aiki.

Wasu kungiyoyin Arewa sun goyi bayan Limamnin na masallaci Apo, suka ce Sa'idu Dansadau ya na da wani buri a ransa da har ta sa ya dauki irin wannan matakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel