Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Sifetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Yayin Da Suke Sallah a Masallaci

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Sifetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Yayin Da Suke Sallah a Masallaci

  • Wasu hatsabiban yan bindiga sun kutsa masallaci sun sace limamin masallacin, wanda sifeta ne a rundunar yan sanda a Ogun da wasu mutum uku
  • Bayanai sun nuna cewa daga bisani an sako jami'in dan sandan da mutane ukun bayan biyan wani adadin kudi a matsayin na fansar su
  • Kakakin yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da sakin mutanen da aka yi garkuwar da su amma bai da masaniya kan batun biyan kudi

Jihar Ogun - Ƴan bindiga sun sace wani sifetan yan sanda da wasu mutane biyu a cikin masallaci a unguwar Soyeye a Abeokuta ranar Lahadi da ta gabata.

Tribune Online ta rahoto cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8 na dare a lokacin da wadanda abin ya faru da su suke sallah.

Kara karanta wannan

Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna, ya zuba jami'an tsaro

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Siften Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Yayin Da Suke Sallah a Masallaci
'YYan Bindiga Sun Sace Siften Ƴan Sanda Da Wasu Mutum 3 a Masallacin Ondo. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: UGC

Sifetan yan sandan, Kamordeen Bello, kafin sace shi yana aiki ne tare da hedkwatar yan sanda a babban birnin jihar kuma shine limamin masallacin.

Ba a tabbatar da adadin kudin da masu garkuwar suka karba ba

Masu garkuwan sun bukaci a ba biya su Naira miliyan 5 a kan kowanne cikinsu daga iyalansu kafin su sako su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano cewa an sako wadanda abin ya faru cikin makon da ta gabata bayan an biya wani kudi da ba a san adadinsa ba.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai tabbatar an biya kudi kafin a sako su ba.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari a Kaduna, Ana Fargabar Sun Kashe Mutane Da Dama

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel