Jigawa: Mutane 9 Sun Mutu a Mummunan Haɗarin Mota, 50 Sun Jikkata

Jigawa: Mutane 9 Sun Mutu a Mummunan Haɗarin Mota, 50 Sun Jikkata

  • Hukumar kiyaye hadurran titi ta Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 9 sakamakon hadarin motan da ya auku a karamar hukumar Ringim
  • Sannan rundunar ta tabbatar da cewa mutane 50 ne suka samu raunuka a wurare daban-daban a titin Ringim zuwa Chaichai kusa da titin Kwanar Shafar
  • Hadarin ya auku ne da misalin karfe 6:23 na safe wanda hakan yasa aka zarce ce a mutanen babban asibitin Ringin don su samu kulawa kamar yadda Kakakin rundunar ya shaida

Jigawa - A ranar Juma’a hukumar kiyaye hadurran titina reshen Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 9 sakamakon hadarin motan da ya auku a karamar hukumar Ringim.

Sannan akalla mutane 50 ne suka raunana sakamakon hadarin da ya auku da misalin karfe 6:15 na safe a hanyar Ringim zuwa Chaichai kusa da hanyar Kwanar Shafar, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

‘Yan Hisbah sun kama litoci fiye da 2000 na burkutu da kwalaben giya 96 a Jigawa

Jigawa: Mutane 9 Sun Mutu a Mummunan Haɗarin Mota, 50 Sun Jikkata
Mutane 9 Sun Mutu a Mummunan Haɗarin Mota a Jigawa, 50 Sun Jikkata. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Rundunar ta shaida yadda aka kai mata rahoto da misalin karfe 6:23 na safe wanda hakan yasa aka zarce da marasa lafiyar babban asibitin Ringim don duba lafiyarsu.

Kakakin rundunar, Ibrahim Gambo ya sanar da NAN cewa hadarin ya ritsa da mutane 70 ne wanda ya auku da mota mai lambar rijista TAR 357XA, wacce wani Babangida Muhammad ne ya tuko.

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, Gambo ya alakanta hadarin da kin kiyaye dokokin titi da dayan direban ya yi.

Direban ne ya rikice ne daga nan motar ta kubuce masa ta fadi

Sai dai mutane 13 sun rasa rayukan yayin da sauran mutane 32 suka raunana.

Jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tashin hankali yayin da tankar gas ta fashe a kusa da wani banki

“A ranar 1 ga watan Afirilu da misalin karfe 6:30 na safe muka samu labarain yadda wata tirela mai lambar rijista, TAR 357 wacce wani Babangida Mohammed ya tuko ta ke cike makil da mutane 53, shanu da awaki tun daga karamar hukumar Maigatari inda suka doshi Jihar Legas, ta tafka hatsari.
“Direban ya rasa yadda zai yi yayin da ya kai Kwanar Shafar da ke wuraren Ringim hakan yasa tirelar ta kubuce daga hannunsa ta fadi.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel