‘Yan Hisbah sun kama litoci fiye da 2000 na burkutu da kwalaben giya 96 a Jigawa

‘Yan Hisbah sun kama litoci fiye da 2000 na burkutu da kwalaben giya 96 a Jigawa

  • Rundunar Hisbah a jihar Jigawa ta kama wani mutumi da aka samu da kayan barasa
  • Shugaban jami’an Hisbah na reshen ya bayyana cewa abin ya faru ne a garin Maigatari
  • Sojojin hukumar sun ce sun samu garwowi 8 na burkutu da kwalabe kusan 100 na giya

Jigawa - Rundunar Hisbah na reshen jihar Jigawa ta bayyana cewa ta yi nasarar yin ram da wasu kayan barasa a makon nan.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Laraba, 30 ga watan Maris 2022 cewa wannan abin ya faru ne a karamar hukumar Maigatari.

Hukumar ta ce jami’anta sun karbe duro takwas masu cin lita 25 cike da giyar hatsi ta gargajiya wanda aka fi sani da burkutu.

Bayan haka, dakarun na Hisbah masu kokarin dabakka shari’ar addinin musulunci sun yi ram da kwalaben giya a wannan garin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka jama'a masu yawa a sabon harin da suka kai Benue

Jaridar Daily Post a rahoton da ta fitar, ta bayyana cewa kwalabe 96 na kwalaben giya aka kama a yammacin ranar Talatar nan.

Shugaban Hisbah ya zanta da 'yan jarida

Shugaban dakarun Hisbah na reshen jihar Jigawa, Ibrahim Dahiru Garki, ya shaidawa hukumar dilllacin labarai wannan a jiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu giya
Wasu mashaya giya a Najeriya Hoto: business247news.com
Asali: UGC

Garba Bakule ya shiga hannu

Malam Ibrahim Dahiru Garki ya bayyana cewa sojojin Hisbah sun kai wani samame na musamman da karfe 3:00 na dare.

A cewar shugaban ‘yan Hisbah na reshen jihar, an kama wani mutum mai suna Garba Bakule ne dauke da wadannan kayan barasa.

Ibrahim Dahiru Garki ya sha alwashin cewa jami’an Hisbah za su cigaba da kokari wajen ganin an yi maganin tsageru a al’umma.

An rahoto Malam Garki a madadin dakarun yana yabawa mutanen jihar Jigawa da gudumuwa da hadin-kan da suke ba hukumar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Kawo yanzu an kai Bakule ofishin ‘yan sanda a garin domin a bincike shi. Daga nan ana sa ran cewa za a gurfanar da shi a kotu.

Talakawan Najeriya za su karu

Dazu aka ji labari cewa babban bankin Duniya ya ce an dauki lokaci ba a iya tsamar da al'umma daga kangin talauci a Najeriya ba.

Hasashe ya nuna talakawan da su ke zaune a kasar Najeriya sun kara yawa, sun doshi miliyan 95.1 a dalilin annobar Coronavirus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel