Da Duminsa: Tashin hankali yayin da tankar gas ta fashe a kusa da wani banki

Da Duminsa: Tashin hankali yayin da tankar gas ta fashe a kusa da wani banki

  • An yi mummunan hadari a jihar Ogun, lamarin da ya haifar da hargitsi tsakanin mazauna Mowe na jihar
  • An ruwaito cewa, wata tankar dakon iskar gas ce ta fashe a kusa da wani banki da ke yankin na Mowe
  • Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana irin asarar da aka tafka ba; ta rai ko dukiya, domin hukumar kashe gobara bata yi karin bayani ba

Ogun - Wani rahoto mai tada hankali na cewa an samu fashewar wata tankar iskar gas a yankin Mowe na jihar Ogun a daren ranar Lahadi, 27 ga watan Maris.

Fashewar da ta faru da misalin karfe 10 na dare ta haifar da tashin hankali da hargitsi a tsakanin mazauna yankin, inji rahoton Punch.

Gobara ta tashi a jihar Ogun
Da Duminsa: Tashin hankali yayin da tankar gas ta fashe a kusa da wani banki | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Rahoton ya kara da cewa, gobarar ta tashi ne a kusa da wani ginin bankin First Bank da ke unguwar Mowe a hanyar Legas zuwa Ibadan.

Kara karanta wannan

An yankewa wacce ta raba man fetur a taro hukuncin watanni 27 a gidan yari

Da take tabbatar da afkuwar lamarin, mai magana da yawun hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta ce an tura jami’anta zuwa wurin domin kashe wutar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Okpe ya ce:

“Fashewar tankar iskar gas ce. Tawagar cetonmu tana can tuni. Zan muku karin bayani daga baya."

Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

A baya, mummunar gobara ta tashi inda ta kone kadarorin miliyoyin naira a kwalejin First Ladies da ke Mariri a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Ana amfani da ginin ne a matsayin wurin adana kayayyaki na hukumar taimakon gaggawa, SEMA na jihar Kano, kuma gobarar ta taba wasu sassan makarantar, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin bada labarin, sakataren SEMA, Dr Saleh Aliyu Jili ya ce kayan rage radadin sun hada da katifu da matasan kai 900, injinan markade, keken dinki, injinan faci, omon wanki da sauransu duk gobarar ta lamushe.

Kara karanta wannan

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

Ya ce kayayyakin da suka kone duk an karbo su ne daga gwamnatin tarayya domin taimakawa 'yan gudun hijira.

Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni

A wani labari na daban, wata gagarumar gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Gamboru Ngala a jihar Borno, lamarin da yasa daruruwan 'yan gudun hijiran suka rasa matsuguni.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya auku da yammacin Lahadi inda gobarar ta lamushe wurare masu tarin yawa a sansanin.

Wani jami'in hukumar taimakon gaggawa ta jihar, SEMA, da ke Gamboru Ngala, Malam Yusuf Gulumba, ya sanar da Daily Trust cewa an fara binciken abinda ya kawo gobarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel