Minista ya saba alkawari, ya ce aikin Ajaokuta da ake jira tun 1979 ba zai kammalu a 2023 ba

Minista ya saba alkawari, ya ce aikin Ajaokuta da ake jira tun 1979 ba zai kammalu a 2023 ba

  • Gwamnatin tarayya ta hakura da batun tada kamfanin karafunan Ajaokuta steel plant kafin shekarar badi
  • Minista Olamilekan Adegbite ya ce annobar COVID-19 da rikicin Rasha v Ukraine sun kawowa Najeriya cikas
  • Da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, Olamilekan Adegbite ya ce abin da kamar wahala

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ba zai yiwu a gama aikin farfado da kamfanin karafunan Ajaokuta steel plant a 2022 kamar yadda aka yi alkawari ba.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto a ranar Alhamis inda aka ji Ministan ma’adanan tarayya, Olamilekan Adegbite, yana bada uzurin rashin cika alkawarin.

Olamilekan Adegbite ya ce yakin da ya barke tsakanin Rasha da kasar Ukraine ya jawo Najeriya ta gagara yin wannan aiki kamar yadda aka yi niyya tun farko,

Kara karanta wannan

Shugaban Nijar ya ba Buhari shawarin yadda za a magance matsalar tsaro a Arewa maso yamma

A cewar Adegbite, kafin annobar COVID-19, gwamnatin Muhammadu Buhari tayi nasarar shawo kan kasar Rasha wajen ganin ta karasa aikin wannan kamfani.

Magana ta watse bayan COVID-19

Amma ba a iya cigaba da tattaunawa da yarjejeniyar da za a bi wajen aikin ba, sai yaki ya barke. Adegbite ya shaidawa ‘yan jarida wannan a fadar Aso Rock.

Yarjejeniyar aikin za ta ci Dala miliyan 2 na bincike domin ganin ko zai yiwu a soma yin aikin.

Ajaokuta Steel
Kamfanin Ajaokuta Steel Plant a jihar Kogi Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Sai dai bayan mun tafi - Minista

Farawar yakin Rasha da Ukraine ke da wuya sai komai ya jagwalgwale. Amma Minista ya yi alkawarin za a iya magana ta yadda za a soma aikin bayan 2023.

Za a shiga wata yarjejeniya da ba za a iya warware ta ba, ta yadda ko bayan shudewar gwamnatin Muhammadu Buhari, Najeriya za ta ci moriyar wannan aikin.

Kara karanta wannan

Muna alfahari: Gwamnatin Buhari ta ji dadin yadda 'yan Najeriya ke more tafiya a jirgin kasa

“A halin da mu ke ciki a yau, ba za mu iya ganin an tado da kamfanin Ajaokuta ba, amma ina addu’a mu fara aikin da zai dore har abada.”
“Na fada a baya, lokacin da mu ka dawo daga Rasha, na fadawa jama’a cewa za mu kammala aikin farfado da Ajaokuta kafin wa’adinmu.”
“Ina addu’a in samu damar da zan koma in bada hakuri, in yi wa jama’a bayanin abin da ya faru kafin in bar ofis.” - Olamilekan Adegbite.

An rahoto Ministan kasar yana cewa ba laifinsa ba ne, annobar COVID-19 ta birkita lissafi. A ka'idar kwangila, ana samun abin da zai so ya fi karfin gwamnati ko hukuma.

Talauci ya na cigaba da karuwa

A wani rahoto da mu ka fitar, an ji cewa duk da Gwamnati ta yi alkawarin ceto miliyoyin mutane daga talauci, amma bincike ya na nuna talakawan kara yawa suke yi.

Kara karanta wannan

Sakon kungiyar Izala ga Buhari: Bai kamata ka bari ASUU su ci gaba da yajin aikin ba

Rahoton bankin Duniya ya nuna abubuwan sun soma yin kyau a shekarar 2010, amma tun daga 2015 sai tattalin arzikin Najeriya ya jagwalgwale, talauci ya karu sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel