Labari mai zafi: Miyagun ‘Yan bindiga sun dawo hanyar Abuja-Kaduna, matafiya sun 'tsere'

Labari mai zafi: Miyagun ‘Yan bindiga sun dawo hanyar Abuja-Kaduna, matafiya sun 'tsere'

  • ‘Yan bindiga sun dawo kan titin Abuja zuwa garin Kaduna, su na neman tare matafiya
  • Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ne ya tabbatar da wannan labarin a shafin Twitter
  • Kawo yanzu babu labarin ko an hallaka mutane, ko an yi garkuwa da wasu mutanen

Rahotanni su na zuwa mana cewa ‘yan bindiga sun tare hanyar garin Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda mu ka ji, ‘yan bindiga barkatai sun yi shinge domin su aukawa matafiyan da ke zuwa garin Abuja.

Sanata Shehu Sani ya tabbatar da wannan mummunan labari a shafinsa na Twitter a yammacin Alhamis dinnan.

Tsohon ‘dan majalisar ya ce an sanar da shi cewa dinbin ‘yan bindiga sun kuma kai hari a wannan hanya a yau.

A cewar Sanatan, fasinjoji da matafiya su na yin baya domin gujewa aukawa tarkon wadannan miyagun mutanen.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Mun san inda 'yan bindiga suke, abu daya ne ya hana mu farmaki maboyarsu

“Yanzu na samu kiran waya cewa ‘yan bindiga masu dinbin yawa sun sake tare titin Kaduna-Abuja da ranar nan.”
Shehu Sani
Maganar Shehu Sani Hoto: @ShehuSani
Asali: Twitter
“Matafiya su na ta komawa baya a guje.” - Sanata Shehu Sani

Zuwa yanzu Shehu Sani bai iya yi wani karin haske a game da harin ba. Kuma daga bakinsa kadai aka ji labarin.

‘Dan siyasar ya yi shagube ga jami’an tsaro bayan an ji sun fara gano mafakar ‘yan ta’adda, ya ce ai sun makara.

Legit.ng Hausa ba ta da labarin ko ‘yan bindigan sun yi nasarar yin garkuwa da mutane ko sun hallaka matafiya.

Mun tuntubi wani Bawan Allah wanda ya bi hanyar dazu, amma har ya sauka ba su gamu da wata matsala ba.

Hari bayan hari

Harin na zuwa ne kwanaki hudu bayan ‘yan ta’adda sun kai mummunan hari ga jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

An ji cewa Majalisa ta aikawa Ministocin tsaro, sufuri da na harkokin jirgin sama gayyata na musamman a jiya,

'Yan majalisa sun nemi manyan gwamnatin su yi bayanin abin da ya faru, amma duk sai su ka turo wasu wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel