Harin jirgin kasa: ‘Yan Majalisar Tarayya sun fusata da 'rainin wayon’ IGP da Ministocin Buhari

Harin jirgin kasa: ‘Yan Majalisar Tarayya sun fusata da 'rainin wayon’ IGP da Ministocin Buhari

  • Majalisa ta aikawa NSA, Ministocin tsaro, sufuri da na harkokin jirgin sama gayyata na musamman
  • Sannan ‘yan majalisar kasar sun nemi jin ta bakin wasu hafsoshin tsaro amma ba su iya amsa kiran ba
  • Shugabannin FAAN, NAMA, da kuma NRC duk ba su samu zuwa ba, sai dai su ka aiko da wakilansu

Abuja - ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun nuna rashin jin dadinsu a game da dabi’ar wasu daga cikin shugabannin hukumomin gwamnati da jami’an tsaro.

Jaridar The Cable ta ce hakan ya biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ne inda har aka hallaka Bayin Allah da-dama.

Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Idris Wase ya yi magana a jiya a kan gazawar manyan gwamnati wajen amsa gayyatar da aka aika masu.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

‘Yan majalisa sun gayyaci Babagana Monguno, Ministan tsaro, Bashir Magashi, Isiaka Amao da Yusuf Bichi na DSS domin su yi bayani kan harin jirgin kasan.

Sannan kuma an nemi jin ta bakin Ministocin sufuri da na harkar jirgin sama, Rotimi Amaechi, Hadi Sirika da kuma shugaban ‘yan sandan kasa, Usman Baba.

Hukumomi sun yi burus

Haka zalika an aikawa shugabannin hukumomin tarayya na FAAN, NAMA, da NRC gayyata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan Majalisar Tarayya
'Yan majalisar wakilan tarayya Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

A karshe wadannan mutane sun turo wakilai ne domin su wakilce su a zauren majalisar kasar.

Hon. Idris Wase ya ji haushin yadda duk suka aiko da wakilai, a maimakon su zo da kansu domin su amsa tambayoyin, don haka aka ki sauran wakilan na su.

An rahoto Wase yana cewa bai raina karfin wadanda aka turo su yi wakilci ba, amma a matsayinsa na mataimakin shugaban majalisa, ba zai saurare su ba.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

“Ina magana ne da bakar zuciya, duk abin da manyan sojojinmu suke yi, na yi imani ya kamata su saurari ‘yan majalisar tarayya, wannan majalisar jama’a ce.”
“Ba na jin dadin yadda na ke bayyana irin jin haushin da mu ka yi.” - Hon. Idris Wase.

Babu uzurin da su ke da shi - Wase

Sannan kuma Wase ya ce babu shugaban daya daga cikin hukumar da aka gayyata da ya samu zuwa gabansu, ya ce ba su da wani uzurin da za su gabatar masu.

O.T. Akinjobi wanda ya wakilci Janar Bashir Magashi a zauren ya bayyana cewa mai gidansa ya na zama da Mai girma shugaban kasa ne a daidai wannan lokacin.

Sakacin gwamnatin tarayya

A baya an ji cewa bayanan sirri sun nunawa hukuma cewa ‘yan ta’adda su na shirin kai wannan mummunan hari da aka kai wa matafiya daf da isowa garin Kaduna.

Amma a karshe jami’an tsaro da hukumar NRC ta kasa ba su dauki matakin da ya kamata ba, har ‘yan ta’adda suka yi mugun ta'adin da ya jawo aka rasa mutane barkatai.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel