El-Rufai: Mun san inda 'yan bindiga suke, abu daya ne ya hana mu farmaki maboyarsu

El-Rufai: Mun san inda 'yan bindiga suke, abu daya ne ya hana mu farmaki maboyarsu

  • Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa, gwamnati ta san mafakar 'yan bindiga a kasar nan
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi kan harin da 'yan bindiga suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
  • Gwamnan ya bayyana dalilin da yasa har yanzu ba a dauki mataki kan 'yan bindigan da suka addabi jama'a ba

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i, a ranar Larabar da ta gabata, ya amince da cewa hukumomin Najeriya sun san sansanonin 'yan bindiga kuma suna sauraron tattaunawar 'yan ta'addan da ke addabar yankunan Arewa.

Gwamnan wanda ke magana bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi kai hari kan jirgin kasan Abuja hari a yammacin ranar Litinin, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Gwamna El-Rfuai ya magantu kan batun 'yan bindiga
El-Rufai: Mun san inda 'yan bindiga suke, abu daya ne ya hana mu farmaki maboyarsu | Hoto: dailytrust.com

Akalla mutane takwas ne suka mutu yayin harin wanda ya dauki kusan sa'o'i biyu ana yin shi. Wasu fasinjoji da dama sun samu raunuka na harbin bindiga yayin da har yanzu ba a tantance adadin mutanen da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su ba.

Mallam El-Rufai yana magana ne a wani taron da ya samu halartar ministan sufuri, Rotimi Amaechi, domin yiwa ‘yan Najeriya bayani kan abubuwan da gwamnati ke yi na dakile matsalar ‘yan bindiga a jihar bayan harin na ranar Litinin.

Gwamnan ya bayyana dalilin da yasa sojoji basu kai farmaki kan 'yan bindigan ba duk da sanin inda suke da kuma sauraron hirarsu.

A cewarsa:

“Mun san inda sansaninsu yake. Mun san sansanonin su, muna da taswira; mun san komai. Muna da lambobin wayarsu kuma muna sauraron hirarsu wani lokaci. Amma dole ne a yi shi a fadin jihohi biyar."

Kara karanta wannan

Shugaban UN yayi Allah wadai da harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Dalilin da ya hana a farmaki maboyar 'yan bindiga

Gwamnan ya bayyana cewa tun da farko sojoji sun hakura da farmakar sansanonin ‘yan bindigar ne domin kaucewa illata farar hula amma ya kara da cewa tun da kotun Najeriya ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda yanzu komai ya sauya.

Ya kuma kara da cewa:

"Wannan yaki ne."
“Mun san abin da su (’yan ta’adda) suke shiryawa. Muna samun rahotanni. Matsalar ita ce hukumomi su dauki mataki. Kada ku jira har sai sun kawo hari kafin ku dauki mataki.
"Ya kamata Sojoji su farmaki matsugunin su domin su kakkabe su. A bar sojojin saman su yi ruwan bama bamai,”

Malam El Rufa'i wanda ya fusata ya koka da cewa SSS na da masu kai musu rahotanni a ko'ina suna samun bayanan hukumar, amma har yanzu irin wadannan hare-hare na kara faruwa.

Za mu hadu da Allah

A wani sakon murya da BBC tace ta samo daga hadimin El-Rufai, gwamnan ya bayyana tsoronsa kan yadda Allah zai tambaye shi ya amsa yadda mulki jama'a.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Har yanzu ba a san adadin mutanen da harin jirgin kasa Abuja-Kaduna ya shafa ba

"Hakkin shugabanci kamar yadda malamai da jagoran addinin kirista suka fada, abu ne wanda wata rana zan tsaya gaban Allah SWT in yi bayanin me na yi don tabbatar waɗannan abubuwa ba su faru ba.
"Ina tsoron wannan rana da zan tsaya a gaban Allah na fadi me na yi, me zan iya cewa mun yi? Saboda haka dole mu roƙi gafararku da afuwarku domin a gwamnatance mu muka kasa.
"Kuma al'umma da laifinku, amma zan zo kanku tukunna."

Kaduna: Tashin hankali yayin da mazauna suka tsinci bam a kusa da wani rafi

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta dakile yiwuwar tashin wani harin bam da aka dasa a yankin Shanono da ke unguwar Rigasa a karamar hukumar Igabi a jihar.

Rahotanni sun ce an boye na’urar ne a cikin wani bokiti kana aka jefar da kusa da wani rafi da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Alhamis 31 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari

Wani mazaunin yankin mai suna Tijjani Haruna Shehu ya shaida wa Daily Trust, cewa an rufe bokitin ne da salatef wanda ya sa mutanen da ke kusa da wurin suka fara nuna shakku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel